Ba za mu lamunci shigar 'yan Nijar harkokin zabe ba — PDP
Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya PDP, ta yi korafi kan zuwan gwamnan jihar Maradi da na Damagaram a jamhuriyar Nijar taron yakin neman zaben shugaban kasar Muhammadu Buhari a Kano.
Sakataren jam'iyyar ta PDP na kasa Sanata Umaru Tsauri, ya shaida wa BBC cewa, sun 'yan PDP, sun kalli zuwan gwamnonin Nijar da ma wasu al'ummar kasar zuwa kaddamar da yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari na APC, a wani abu mai ban takaici da haushi kuma mai ban tsoro.
Sanatan ya ce, wannan lamari 'yan Najeriya ba za su amince da shi ba.
A saboda haka, sakataren jam'iyyar ya ce, yakamata hukumomin tsaro su yi karin bayani a kan zuwan 'yan Nijar din wajen taron siyasar Najeriya.
Sanata Tsauri, ya ce babban tashin hankalin da suka gani shi ne sun ga motocin yakin neman zaben shugaban kasar Nijar na dauke da hotunan shugaba buhari.
Ya ce wannan lamari abin mamaki ne, domin ba a taba samun irin haka ba a duniya.
Sakataren jam'iyyar ta PDP, ya ce 'Babban abin fargabar shi ne wannan abu da aka aikata, ya nuna cewa 'yan Nijar za su shigo cikin Najeriya su jefa kuri'a a lokacin zabe'.
Sanatan ya ce, idan kuwa har hakan ta tabbata cewa 'yan Nijar sun jefa kuri'a a Najeriya a lokacin zabe, to za a ja wa 'yan Najeriya tashin hankalin da ba bu wanda ya san karshensa
No comments