5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Za a hade Facebook Whatsapp da Instagram wuri daya - Arew@Blog Za a hade Facebook Whatsapp da Instagram wuri daya - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Za a hade Facebook Whatsapp da Instagram wuri daya

Hadewar su zai sa a rika tura sakonni tsakanin manhajojin uku
Kamfanin Facebook ya bayyana shirinsa na hade shafin da kuma Whatsapp da Instagram duka wuri daya.






Wannan zai bada dama ga masu amfani da shafukan daban-daban su rika zumunta ko tura sakwanni ko da kuwa mutum yana da rajista da manhaja daya zai iya zumunta da wadanda ke amfani da sauran.

Misali, idan mutum yana amfani da Facebook, sai abokinsa yana amfani da Instagram kadai, za su iya zumunci ko tura sako tsakaninsu.
Shafukan da ke zaman kansu, hadewarsu zai sa a rika tura sakwanni tsakaninsu.





Facebook dai shaidawa BBC cewa wannan shirin da sauran aiki a gaba domin yanzu aka fara.
Jaridar New York Times ce ta fara wallafa wannan labarin kuma ana sa ran cewa mai kamfanin na Facebook Mark Zuckerberg ne ya fito da wannan sabon tsarin.





Kamar yadda jaridar ta New York times ta wallafa, an riga an fara wannan aikin kuma ana sa ran za a kamala shi zuwa karshen wannan shekara ko kuma farkon shekara mai zuwa.

No comments

Powered by Blogger.