Tambuwal: Ban taba neman mataimakin shugaban kasa ba
Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana wa BBC dalilansa na ficewa daga jam'iyyar APC da dangantakarsa da Shugaba Muhammadu Buhari a cikin wannan hirar da yayi da BBC.
Ya tabo batutuwa da dama da suka hada da tsayawarsa takarar shugaban kasa, da tsaro a yankin arewacin Najeriya.
Dalilinsa na shiga hadakar da ta samar da jam'iyyar APC:
"Abin da yasa muka shiga hadaka aka kafa jam'iyyar APC, a hijira 2013 zuwa 2015, shi ne domin shawo kan wasu matsaloli da ke gabanmu a matsayinmu na 'yan Najeriya. Matsaloli musamman na tsaro da na yaki da rashawa, da wadanda suka shafi tattalin arziki da kuma tattalin arziki da rayuwar matasa da mata."
Dalilansa na ficewa daga APC:
"Sai abubuwa suka shiga tabarbarewa, yanayi ya kawo har kowa ya san yadda ake gudanar da yaki da cin hanci da rashawa a Najeria akwai gyara. Kowa ya san matsalolin tsaro na son mamaye yankin arewacin Najeriya baki daya."
Dagantakarsa da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari:
"Har Baitul Muqaddas na je na sa goshi na a kasa, na rokan ma iyayena rahama, na rokar wa Muhammadu Buhari lafiya."
Batun neman kujerar mataimakin shugaban kasa a lokacin da Shugaba Buhari ke jinya a birnin Landan:
"Allah, wanda raina ke hannunsa... Ban taba zuwa inda wani mahaluki na nemi mataimakin shugaban kasa ba. Ban taba rokon Allah Ya ba ni mataimakin shugaban kasa ba."
Sai ku latsa alamar lasifika domin jin cikakkiyar hirar da muka nado dominku.
No comments