Mai Dakin Gwamnan Jihar Jigawa Ta Baiwa Mata A Kazaure Tallafin Naira Milyan 57 Domin Bunkasa Sana'oinsu
Daga Engr Magaji Abdullahi Mallammadori
Matar Gwamnan Jihar Jigawa Hajiya Hasina Muhammad Badaru Abubakar a Laraban nan a Ƙaramar Hukumar Kazaure, ta tallafawa mata 11, 400 masu ƙananan sanaa'o'i daga Ƙananan Hukumomi na Shiyyar Arewa maso Yammacin Jihar Jigawa da jarin naira milyan 57 domin bunƙasa sanaa'o'i da kasuwancin su.
A jawabin ta wajen bikin bada tallafin, Hajiya Badaru Abubakar tace ta bada wannan tallafi ne domin bunƙasa ƙananan sanaa'o'i da kasuwancin su domin inganta rayuwar su.
Matar Gwamnan tace mata daga Ƙananan Hukumomin Jihar zasu ci moriyar irin wannan tallafi.
Tayi alƙawarin cewa "Mun fara ne da mata daga wannan shiyya, daga Ƙaramar Hukumar Kazaure, kuma zamu faɗaɗa shirin zuwa sauran mata a dukkan sassan jihar."
Tace a yau an fara tallafawa mata ne da suka fito daga Ƙananan Hukumomin Ringim, Kazaure, Gwiwa, Garki, Babura, Yankwashi, Roni, Maigatari, Gagarawa da Taura, inda kowace mace ta samu tallafin ₦5, 000 domin ƙara jari a Ƙananan sanaa'o'in su, inda tace tana da yaƙinin cewa tallafin zai taimaka wajen rage raɗaɗin talauci a tsakanin al'uma.
A jawabin sa, Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Muhammad Badaru Abubakar wanda ya samu wakilcin mai taimaka masa na musamman akan tallafawa al'uma, Abba Sheikh Mujaddadi, ya yabawa Hajiya Hasina Badaru bisa irin wannan ƙoƙari da tayi, inda yace hakan zai taimakawa ƙudirin gwamnati na tallafawa al'uma a jihar.
A nan ne yayi kira ga waɗanda suka ci moriyar shirin suyi amfani da tallafin ta hanyoyi masu aiki domin inganta rayuwar su.
No comments