5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Ko Mai Yake Tsakanin Nafisa Abdullahi Da Hadiza Gabon? - Arew@Blog Ko Mai Yake Tsakanin Nafisa Abdullahi Da Hadiza Gabon? - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Ko Mai Yake Tsakanin Nafisa Abdullahi Da Hadiza Gabon?

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi, ta ce tana zaune da kowacce jaruma ne “a kan yadda take so su zauna.”
Nafisa, ta yi wannan bayani ne, a cikin wata hira da ta yi da BBC a kwanakin baya.
Jarumar ta ce, “duk wadda ke son zama da ita lafiya lau, to za su zauna lafiya, wadda kuma ke da akasin hakan to takan tafiyarta da ita a kan yadda take so.”






Ta ce ita yanzu a tsakaninta da ‘yan fim, “babu wadda ba sa zaman lafiya.”
Jarumar ta kuma yi karin haske a kan dangantakarsu da jaruma Hadiza Gabon, wadda suka samu sabani a baya.

Ta ce bayan sabanin da suka samu a baya, a yanzu sun fahimci juna.
Nafisa ta ce, “ko da yake ba mu cika haduwa ba, idan dai har mun hadu muna gaisawa.”
“Tsammanin da mutane ke yi na cewa har yanzu muna gaba da juna, wannan ya kau,” in ji ‘yar wasan.
Ta ce “dama shi zaman duniya idan dai har ana tare to wata rana dole a samu sabani, domin ko harshe da hakori ma su kan saba.”






A shekarar 2017 ne fitattun jaruman biyu suka yi fada inda wasu rahotanni suka ce har da duka yayin da suke tsakar shirya wani fim.
BBCHAUSA

No comments

Powered by Blogger.