Yaki Da Boko Haram: Buratai Ya Nemi Hadin Kan Kafafen Watsa Labarai
Shugaban Hafsan Sojojin Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai, ya yi kira ga kafafen watsa labarai akan su baiwa Sojoji goyon baya domin kawo karshen ta’ddancin Boko Haram. Buratai ya yi wannan kiran ne a lokacin wani taro da Editoci da masu aika rahotanni akan al’amarin tsaro suka shirya a Maiduguri. Ya ce; wannan kiran ya zama dole domin duba da yadda ake amfani da farfaganda wajen dakile nasarorin da Sojoji suke samu wajen yaki da Boko Haram. Buratai ya ce; ‘yan ta’addan sun dage wajen amfani da kafafen watsa labarai wajen yada labarai marasa tushe domin saka shakku a zukatan jama’a da dakushe kokarin Sojojin Nijeriya.
Buratai ya koka dangane da labaran da ake yadawa a kafafen sada zumunta domin ganin an bata sunan Sojojin Nijeriya musamman a irin wannan lokaci da ake fama da matsanancin matsalar tsaro. Buratai ya bayyana zargin da kungiyoyin kare hakkin bil’adama suka yiwa Sojojin akan cewa bayani ne wanda ake neman karkatar da tunanin jama’a. Ya ce; ya kamata ya zama yaki da ta’addanci abu ne wanda yake bukatar hannu da yawa, ya ce; ba yaki ne tsakanin Sojoji da ‘yan ta’adda ba kawai. Ya ce; ya kamata a rika kawo rahotanni yadda yakin ke tafiya ne yadda yake, da kuma kokarin wayar da kan al’umma domin su fahimci halin da ake ciki don sojoji su samu goyon baya. Buratai ya ce; Farfagandar da ‘yan ta’addan ke yadawa a irin wadannan kafafen, ya ce; ba karamar koma baya yake kawo wa a yaki da Boko Haram din ba. Ya ce; farfagandar ta su yana saka tsoro da razana a cikin zuciyar sojojin dake fuskantar Boko Haram din
No comments