5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Wasu dake dauke da muggan makamai sun mamaye garin Tangaza, Jihar Sokoto - Arew@Blog Wasu dake dauke da muggan makamai sun mamaye garin Tangaza, Jihar Sokoto - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Wasu dake dauke da muggan makamai sun mamaye garin Tangaza, Jihar Sokoto

Kungiya da ba a san ko wacce iri ba ce ta mamaye karamar hukumar Tangaza, dake jihar Sokoto.
Kungiyar dai har sun fara karbar haraji daga mazauna wannan gari.
An ce wadannan ‘yan kungiya sukan bi gida-gida suna karbar haraji daga mazauna garin Tangaza da kauyukan dake zagaye da garin ba tare da wani ya iya ce musu komai ba har yanzu.
Wani mazaunin garin ya bayyana cewa wadannan mutanen ya ce suna kama da mutanen kasar Nijar, sannan suna nada rawani a kawunan su dauke da manyan bindigogi. ” Sun mamaye garin Tangaza har sun fara matasa sojojin haya, wato matasa suna horas dasu dabarun yaki a karshe su basu sabbin babura”
” Kowani makiyayi na biya wa shanun sa naira 500 sannan tumakai kuma naira 200. Bayan haka suna hukunta makiyayan da ke fadawa gonakin manoma sannan su dora musu tara.
Shi dai wannan gari na Tangaza da kauyukan da ke zagaye da na da iyaka da wasu garuruwan kasar Nijar da har ma auratayya kan hada su.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sokoto ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa yanzu haka yana hanyar sa na zuwa.

No comments

Powered by Blogger.