Kross ne gaba a cin kofin Zakarun duniya
Dan wasan Real Madrid, Toni Kross
shi ne na daya a yawan lashe kofin Zakarun nahiyoyin duniya a kungiyar,
inda yake da biyar jumulla.
Dan kwallon tawagar Jamus ya yi nasarar lasher na biyar ne, bayan da Real Madrid ta doke Al Ain mai masaukin baki a Abu Dhabi.Hakan ne ya sa ya dara Cristiano Ronaldo mai guda hudu tare da Ramos da Marcelo da Carvajal da Isco da Bale da Benzema da Varane da Keylor Navas da Nacho da kuma Modric.
Kross ya fara cin kofin Zakarun nahiyoyin duniya a shekarar 2013 a lokacin da Bayern Munich ta doke Raja Casablanca a wasan karshe.
Sauran hudun ya dauka a Real Madrid ne, wadda ya koma buga mata tamaula a 2014.
No comments