HAJJI 2019: Saudiyya ta tsara wa mahajjatan kowace kasa lokutan yin dawafi
Kasar Saudiyya ta bada sanarwar kirkiro da wasu sabbin matakai da za su rage cinkoso a Ka’aba, yayin dawafi a lokacin aikin Hajji na 2019.
Wannan mataki kamar yadda mahukuntan kasar suka bayyana, zai rage cinkoso, kamar irin yadda aka fito da matakan rage cinkoso a wuraren jifan Shaidan.
Kafin sabbin matakan, mahajjata kan zarce kai tsaye wurin jifar Shaidan a Mustalifa. Sai dai kuma a yanzu an canja, sakamakon tirmitsitsin da ya faru a lokacin jifar Shaidan a aikin Hajji na 2015, wanda ya haifar da asarar dubban mahajjata.
Mahukuntan kasar sun shigo da tsarin tantebur na lokacin da mahajjatan kowace kasa za su fita su yi jifar Shaidan
Sannan kuma an tsara lokacin kowace kasa mahajjatan ta za su tafi su yi dawafi daga Musdalifa bayan jifar Shaidan.
Sannan kuma an tsara lokacin kowace kasa mahajjatan ta za su tafi su yi dawafi daga Musdalifa bayan jifar Shaidan.
Daga 2019, za a kebe wa mahajjatan kowace kasa lokacin da za su gudanar da dawafi.
Hukumar Kula da Aikin Hajjin Kasashen Afrika da ba su jin Larabci ta Kasar Saudiyya ce ta bayyana wa Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON), jiya Alhamis a Makkah.
Haka kuma kamar yadda Jami’ar Yada Labarai ta NAHCON, Fatima Usara ta bayyana, mahukuntan Saudiyya sun tanaji hukunci mai tsauri a kan duk wanda ya shantake ya zarce wa’adin komawar sa kasar su daga aikin Hajji ko Umra idan ya je.
No comments