Zamu Kashe Daya Mu Bar Daya Yau ~ Inji Masu Garkuwa Da‘Yan Biyun Zamfara
Innalillahi Wa Inna Ilaihir Raji'un!!!
Zamu Kashe Daya Mu Bar Daya Yau ~ Inji Masu Garkuwa Da‘Yan Biyun Zamfara
Daga Ubaidullah Yahaya Kaura
Hankalina Ya tashi Matuka, Nagirgiza Sosai lokacinda Naji audio da Maryar Yan biyu Hasana da Husaina suna Kuka.
Masu garkuwa da ‘yan biyun sun yi ikirarin cewa za su kashesu Yau tunda har aka kasa basu Miliyan Dari N100,00000 da suke nema.
A cikin Audio din da suka sake, ‘Yan biyu suna kuka su na cewa a taimakesu, basu da lafiya kuma kullun sai an yi musu duka da itace, kuma da Yunwa suke kwana, kuma agabansu ake yanke mutane gashi suma ance za a yanke dayansu Yau.
Miliyan Dari ba kananan kudade bane amma idan muka duba cikin manya da kananan Masu kudin ake da su a jahar Zamfara za a iya yin wani abu a tara wadannan kudade domin ceto Rayukan wadannan yara.
Akwai sakamako mai tsoka awajen Allah ga duk wanda ya taka rawa wajen ceto Rayuwar wani.
Allah gamu mun kawo kukanmu gareka, Allah bamuda wata dabara ba mu da wata hanya sai taka Allah, kaceci wadannan ‘Yanmata marayu daga wadannan mutane da su da duk wanda ya ke cikin Matsala.

No comments