WASIYYOYI 5 DAGA MANZON ALLAH(S.A.W)
MANZON ALLAH (s.a.w) yace:
:
"Waye zai karbi wadannan kalmomi
guda 5 daga gareni, yayi Amfani dasu, koya sanar da wanda zaiyi Amfani dasu ???"
:
Sai Abu Huraira (r.a) yace Ni zan karba ya MANZON ALLAH.
:
Sai MANZON ALLAH (s.a.w) ya rike hannuna ya maimaita minsu sai yace;-
:
:
1. "Ka guji aikata #SABO, zaka zamo
wanda yafi kowa bauta a cikin mutane.
:
.
2. "Ka yarda da abinda Allah Ya #BAKA, zakafi kowa Arziqi cikin mutane.
:
.
3. "Ka kyautatawa #MAKWAFCIN ka, zaka
zamo (cikakken) Mumini.
:
.
4. "Kasowa mutane abinda kake SOWA KANKA, zaka kasance (cikakken) Musulmi.
:
.
5. "Kada ka yawaita #DARIYA, domin yawan Dariya na kashe zuciya.
:
@SILSILATUL AHAADIISUS SAHIHA
930.
.
MANZON ALLAH (S.A.W) YACE KA
RIKESU KOKA SANAR DA WANDA ZAIYI AMFANI DA SU.
:
Allah bamu iKon kiyayewa,ya shiga cikin Al'Amuranmu.

No comments