5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Ni Atiku Zan Taimaki Talakawa - Arew@Blog Ni Atiku Zan Taimaki Talakawa - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Ni Atiku Zan Taimaki Talakawa

Cikin Maraici Da Talauci Na Tashi A Rayuwata, Don Haka Ya Zama Dole Gareni Na Taimaki Talakawa, Inji Atiku


Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya fara yakin neman zaben shi a ranar Litinin din da ta gabata ta shafinshi na sada zumunta inda ya fara da bayar da labarin cewa ya taso maraya kuma har sayar da itace yayi.

Ya ce ya sayar da itace a kan titunan garin Jada dake Adamawa amma Allah, ta sanadiyyar Najeriya ya daukakashi.

Yace idan Nijeriya ta ba shi irin wannan damar ya kai yadda yake a yanzu, to shi ma yana da aikin gyara Nijeriyar ta yadda za ta baiwa kowane danta irin waccan dama.

Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su bi shi akan wannan tafiya ta samar da rayuwa me kyau.

Ya ce idan aka zabe shi zai taimakawa kananan da matsakaitan masana’antu miliyan 50.

Ya ce wannan tsari zai samar da ayyuka miliyan 2.5 sannan cikin shekaru 2 mutane miliyan 50 zasu fita daga kangin talauci.

Ya ce kuma akwai wani tsari da zai fito dashi na horas da mata da maza miliyan daya duk shekara akan sana’o’i daban-daban.

Yace akan maganar shirinshi na canja fasalin Najeriya kuma zai samar da yanayin da jihohi da gwamnatin tarayya zasu samu kudin shiga fiye da da.

Ya kara da cewa ga wanda ke so ya karanta tsare-tsaren nashi zai iya yin haka a shafinshi Atiku.org.

No comments

Powered by Blogger.