MACE GUDA DAYA TILO PART 3
7⃣3⃣
Yana shigowa yaga har bacci ya dauketa dan haka kusa da ita ya je yakwanta yashiga cikin jikinta, can cikin dare yaji zazzabi ya rufeta jikinta yayi zafi zau kamar wuta cikeda tausayawa yaja bargo ya rufesu sai dai shi baiyi wani baccin kirki ba motsi kadan zai tashi ya haskata yaga halin da take sannan zai kwanta ana jimawa zai kara tashi da haka har gari ya waye shi tun asuba yayi salla amma bai tasheta ba gudun kar ya katse mata baccinta sai wurin 6 sannan ta tashi yana kwance agefenta ta dan kalleshi sai taga idanuwansa arufe duk azatonta bacci yake dakyar ta iya tashi kamar mai koyon tafiya tafara takawa ahankali ya bude idonsa ya bita da kallo cikeda tausayawa ahaka yaga ta fito ta shimfida sallaya tasa dogon hijabinta har kasa zama tayi saboda ba zata iya tsaiwar ba kwalla ce yaji ta ciko masa ido yayi saurin gogewa ahaka ta idar da sallar ta dawo gadon ta kwanta, kanta ya dago ya kwantar akan kirjinsa yace sannu junada yaya kike jin jikin naki, zazzabi nakeji yana neman rufeni kuma kaina sai ciwo yake sannan jijiyoyin jikina jinsu nake kamar ana tsintsinka min su, cinyoyina kuma kamar ana sassara min gashi sunyi tsami kuma sunyi min nauyi,cikin tausayawa yace sannu bari naje na nemo miki magani, yana fitowa falo yaji ana kwankwasa kofar budewa yaje yayi husna da hasna yagani a tsaye yaya ina kwana lfy ya akayi? Gurin Anty mukazo, me zakuyi mata? Mun jita shiru tun jiyane shiyasa, lafiyar ta lau,Ku koma ku shirya mana breakfast zan zo na karba yana gama fadin haka ya maida kofar ya rufe yashiga dakinsa ya saka jallabiya da dogon wando yafito saida yasa key ya kulle kofar falon sannan yafita motarsa ya dauka ya tafi wani chemist ya siyo mata magunguna sannan ya dawo gidan, side din mummy ya shiga ya dauko kayan breakfast din yashiga side dinsu lokacin har ta tashi daga bacci tayi wanka da ruwan dumi ta gaggasa jikinta babu laifi ta danji dama dama tayi kwalliyar ta cikin wani brown din leshi tana zaune a falo ta kunna kallo, yana shigowa ta sukwi da kanta kasa bata yarda sun hada ido ba gabanta yazo ya ajiye abincin ya zuzzuba mata soyayyiyar doya da kwai da farfesun hanta, sauko da ita yayi ya dorata akan cinyarsa yafara bata abaki gaba daya idonta sunyi jawur fuskarta ta kumbura abinka da farar mace sai kace sweet choco kawata, ahaka har ta koshi ya bata maganin tasha sannan shima ya dan ci abincin ya tashi ya shiga dakinta ya gyara mata ya share ya kunna turaren wuta yadawo falonma ya gyara ya shiga kitchen ya wanke mata kwanuka ya share sannan ya dawo falon da take,kallo kawai take binsa dashi daga shi sai best da gajeren wando.
7⃣4⃣
Falon yadawo ya feffesa air freshener yasaka turaren wuta bugun kofar da yaji ana yine yasashi tashi ya leka su hasna ne cikin shirin tafiya makaranta lekowa yayi yace ya akay? Yaya dama mun shirya ne shine muka biyowa Anty, kuyi tafiyarku ita yau bazata ba sai kun dawo kofar ya mayar ya rufe, wunin ranar dai bai huta ba dukkan ayyukan gidan shine yayi mata har tausayi yabata saboda yanda yaketa nan nan da ita gashi yanada lecture amma duk ya share yaki zuwa shi ta lafiyar matarsa yake. Haka ya rinka bata kulawa har na tsawon sati daya lokacin da ya fuskanci ta warware ne yafara fita kuma aranar ya kawo mata yan aiki guda 3 yace bai yadda tayi kowanne aiki ba in banda girki da gyaran dakinsa,wata soyayya mai wuyar fadi suke nunawa junansu, su husna kuwa tuni sun koma sashen mummy domin abin yafi karfinsu agabansu lamin yake kissing din junada ko ya rungumeta,yauma suna zaune acikin falo dukansu suna kallo ya dawo daga office ko kunyar su baiji ba yaje yashige cikin jikin junada ahankali ya lalubi bakinta yasaka cikin nashi hasna ce tace kinga husna zo mu tafi duk lokacin da suke da bukatarmu sa kiramu hakan kuwa akayi suka tashi suka tafi wurin mummy, ita kuwa junada dama tama manta da suna wurin domin ta dade tana kaunar jajayen lips din lamin dan suna mutukar burgeta. Ahaka rayuwarsu tayi ta tafiya cikin farin ciki alokacinne Kausar suka dawo daga kasar Uganda ita da Abdulrahman cikinta ya tsufa sosai, lokacin itama junada ta soma nata yan jinyace jinyacen da zazzabi ganin abin yayi yawa yasa lamin yakira mata likita har gida yana dubata ya ta tabbatar musu tana dauke da juna biyu na wata 2 tuni lamin yafara murna wai shine zai haifi dan kanshi, murmushi ya saki mai kayatarwa junada tace lfy? Kallonta yayi yace abin ne ya burgeni dalibata zata haifa min yara, murmushin itama tayi tace ai malamin ne akwai iya daukar fansa dariya yayi yajawota jikinsa ya rungumeta yace duk cikin friends dina fa ni kadai ne nayi auri gashi har zan haihu dariya itama tayi tace to ai kayi dabara nasan nice zan rigaka tsufa tunda kai namiji ne murmushi yayi ya kama hannunta yayi kissing dinsa sannan yace no ni yanzu inada 27 ke kinada 21 tare zamu tsufa, malami dai ya auri dalibarsa.
7⃣5⃣
Ahaka ya shagaltar da ita da soyayyarsa mai wuyar fahimta. Washe gari kausar ta haifi yaronta santalele mai kamada lamin sak dan haka ranar suna ma sunan lamin din yayansa yasakawa yaron, yanzu rayuwa tayiwa junada dadi domin ta fahimci ita kadai ce MACE GUDA DAYA TILO acikin zuciyar mijinta yana bata dukkan kulawa kuma ahaka yayita tayata renon cikinta har ya isa haihuwa ranar da zata haihu lamin baya nan dan haka sai dawowa kawai yayi yaga ta haifi jariranta masu kama dashi sak, su husna kuwa tamkar zasu cinye su don so shi kanshi lamin yaran sun shiga ranshi dayawa haka akasha shagalin suna inda yaran sukaci sunan mahaifinsa da mahaifin junada ana kiransu sudais da shurem ansha buduri sosai washe garin suna mami kanwar umman junada ta tafi da ita bauchi tace sai bayan sunyi arba'in zasu dawo lamin kuwa bai so ba dan babu yadda zaiyi ne amma baiso sukayi nesa dashi ba, ita kuwa Mami tayi hakane domin ta samu damar gyara masa ita, duk karshen sati yake zuwa bauchi wurinsu da haka har suka cika arba'in saida suka dan zazzaga dangi sannan suka dawo yola lamin ne yaje dakansa ya daukosu yaci gayu cikin wani farin boyel mai shegen kyau da tsada idan kaganshi bazaka taba cewa yana da mata ba balle har kace ya ajiye yara biyu.
7⃣6⃣
Haka ya debo su yana cike da doki domin shi kansa yasan yayi missing din junada, la'asar lis suka karaso gida cike da tsarabar bauchi su husna sai murna akeyi shi kuwa lamin alla alla yake su kebe shida matarsa domin ya tabbatar mata da cewa yayi rashinta. Ahaka suka ci gaba da rainon yaransu kuma alokacinne aka sanya ranar bikinsu husna zasu auri wasu twins yayan Governor din garin zamfara, dan haka suna gama karatunsu aka fara bikin junada itace uwar biki domin itace akan komai yan biyunta kuwa har sunyi wayo sun girma ba adade da bikinsu hasna ba ta yayesu lokacin sun cika 1 year. Haka suka ci gaba da rayuwarsu cikin farantawa juna tareda kyautatawa junansu ayanzu auren ramuwar gayya yazama auren soyayya. Yau an tashi da sanyi junada ta shirya cikin wani jeans da riga body hug ta dora katuwar riga sanyi asama ta nufi dakin lamin yana kwance yana bacci shida yaransu murmushi tayi ta juya tafice. Da yamma yafito cikin wata riga t. Shirt green da bakin wando ya isketa afalo tayi kyau tamkar wata budurwa ta bayanta yaje ya rungemata tattausan hannunta tasa ta shafo sumar kansa tace naga kayi kwalliya sai ina? Neman aure ai tuni tafara kwalla aure ? Dariya yayi yace dauko gyalenki ki rakani da gudunta ta dauko ta fita ta sameshi a mota shida yan biyu suna jiranta cikin garin yola suka shiga basu zame ko ina ba sai state university yola suna zuwa yafito yashiga cikin hall din inda dalibai sukayi dafifi suna jiransa, test ya rubuta musu yana cikin rubutunne yan biyu suka shigo cikin hall din dagudu sudais ne agaba shurem ya biyoshi cikin muryarsa ta yan yara yace daddy help me pls dagudu yazo ya rungume lamin cikin sauri lamin ya dagashi sama yana fadin wooh! Bai kamaka ba gaba daya yan ajin suka sa dariya wasu kuwa mamaki suke yanzu wannan malamin dama yana da aure? Sun ganshi dan yaro dashi ahaka yagama yi musu test din suka nufo gida akan hanyarsu ta dawowa ne yakalle junada yace yanzu idan akace miki zanyi aure sai ki yarda? Kallonsa tayi tace ehh mana murmushi yayi yace to ni babu auren da nake nema domin ke kadai kin isheni kuma ke kadaice MACE GUDA DAYA TILO acikin zuciyata, kwantar da kanta tayi ajikin kafadarsa tana cewa na gode mijina.
Alhamdulillah!

No comments