Labari Da Dumi-Dumi- Kotu A Jihar Kano Ta Dakatar Da Binciken Ganduje
Labari Da Dumi-Dumi- Kotu A Jihar Kano Ta Dakatar Da Binciken Ganduje
Babban kotun jihar Kano ta dakatar da kwamitin majalisar dokokin jihar Kano kan zargin gwamna Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da karbar makudan rashawa daga hannun ‘yan kwangila.
Dakatarwar ta biyo bayan kara da lauyoyin gwamnati suka shigar a yau Litinin karkashin jagorancin Ahmed Zaubair, inda lauyan ya nemi kotu da ta dakatar da binciken da ake yi wa mai girma gwamnan.
Alkalin Kotun AT Othman, ya karbi korafin da aka shigar, inda ya umarci Kwmitin majalisar dokokin jihar da su dakatar da bincikensu ga Gwamna Abdullahi Ganduje.

No comments