5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 DAN AUTAN SULE LAMIDO YACE IDAN KAZAGI SULE LAMIDO UBANA KA ZAGA - Arew@Blog DAN AUTAN SULE LAMIDO YACE IDAN KAZAGI SULE LAMIDO UBANA KA ZAGA - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

DAN AUTAN SULE LAMIDO YACE IDAN KAZAGI SULE LAMIDO UBANA KA ZAGA



Daga: Dan Autan Sule Lamido

Da ranar yau, mai girma Gwamnan jihar Jigawa, Alh. Muhd Badaru Abubakar, ya karbi bakoncin tsofin wakilan kungiyar Sule Lamido social media, daga kananan hukumomi 27 dake fadin jihar.

Shugaban tafiyar, Engr, ya bayyana wa gwamnan, wannan ziyara ce da  wannan 'yan tsohuwar waccar kungiya suka kawo wa gwamnan, da kuma tabbatar da biyayyarsu ga wannan Gwamnatin, na ganin irin aiyukan alkhairi da take bulbulawa. Sa'id ya bayyana nawa gwamnan, cewa sun kafa sabuwar kungiya domin aiki tukuru, (APC NEW MEDIA FRONT)/wajen ganin wannan adalar gwamnati ta kai ga nasara.

Gwamnan jihar Jigawa, Alh. Muhammad Badaru Abubakar, ya yaba wa wannan 'yan kungiya, bisa irin wannan hangen nesa da sukai tun wuri.

Gwamnan ya ja hankalin 'yan kungiyar da su guji cin mutuncin shugabannin su, domin "Sule Lamido ubana ne, in ka zagi Sule Lamido wallahi ni ka zaga" in ji Gwamna Badaru.

Gwamnan ya ce ya yafewa duk wani wanda ya bata wa a baya, kuma ya nemi yafiyar duk ka wanda ya batawa shi ma.

Daga karshe Gwamnan ya yi wa kowa fatan alkhairi, da kuma zage damtse domin aiki tukuru.

No comments

Powered by Blogger.