Shin ko Obasanjo ya ce a zabi Buhari, kada a zabi Atiku a 2019?
Tun bayan da babbar jam'iyyar adawa a
Najeriya PDP ta tsayar da Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takarar
shugaban kasa a zaben 2019, jama'a suke ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu
game da dan siyasar musamman a kafofin sada zumunta a kasar.
Yayin
da wadansu suke ganin tsohon mataimakin shugaban kasar zai iya doke
Shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC, wasu suna ganin hakan ba mai
yiwu ba ne. Wannan batun shi ne abin da ya mamaye shafukan sada zumunta a Najeriya tun bayan da manyan jam'iyyun kasar biyu suka sanar da sunayen wadannan 'yan siyasan.
Jama'a sun rika yada labarai musamman game da Alhaji Atiku Abubakar wadanda ba sahihai ba ne, ciki har da wadanda ake ikirarin cewa wai sun fito ne daga kafar yada labarai ta BBC.
Da gaske ne Obasanjo ya ce a zabi Buhari, kuma kada a zabi Atiku?
An rika yada labaran karya a kafofin sada zumunta inda ake cewa tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya bukaci 'yan kasar da su zabi Shugaba Buhari a zaben 2019, kuma Atiku ba zai taba yin shugabancin kasar ba.
Atiku, wanda ya yi wa Obasanjo mataimakin shugaban kasa tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007, bai taba samun goyon bayansa ba a fafutikar da ya sha yi a baya na neman takarar shugabancin kasar.
Kodayake Shugaba Buhari ya samu goyon bayan Mista Obasanjo a lokacin da ya lashe zaben 2015, amma daga bisani a bana, ya bayyana cewa ba ya goyon bayan tazarcen shugaban.
BBC ba ta yi wata hira da Mista Obasanjo ba kan zaben 2019, hakazalika babu wani labari mai kama da wannan da kafar yada labaran ta ruwaito.
Shin Atiku ya kai ziyara Amurka har ya gana da Trump?
A wata hira da BBC ta yi da Alhaji Atiku Abubakar game da neman takararsa a zaben 2019 wanda aka yi da shi a ofishinmu na Landan a bana.
Editan sashen Hausa Jimeh Saleh ya tambaye shi dalilin da ya hana shi zuwa kasar Amurka, inda Atikun ya ce bai san dalilin da ya sa kasar ta hana shi Biza ba.
Shi ma wannan batun ya ba da wata kafa ta yada wasu labaran kanzon kurege a kafofin sada zumunta.
An rika wallafa wani hoton boge a shafin sada zumunta inda ake ikirarin nuna dan siyasar yana gaisawa da Shugaba Donald Trump a gaban fadar White House bayan taron manema labarai.
Ko jikar Atiku ta ce 'Sai Buhari'?



No comments