5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Kano: Wai Yaushe Talakawa Za Mu Yi Hankali Ne? - Arew@Blog Kano: Wai Yaushe Talakawa Za Mu Yi Hankali Ne? - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Kano: Wai Yaushe Talakawa Za Mu Yi Hankali Ne?



Daga Aliyu Usman Adam



A gaskiya abun da ya faru a Kano yau abun takaici ne da bakin ciki ta yadda aka sanya yara dauke da kwalaye suna nuna goyon bayansu kan abun da ba su san ma'anarsa ba.

Iyayen yara sun tura 'ya'yansu makaranta don su yi karatu amma malaman makarantu suka dauki yaran nan aka tafi da su zanga-zanga don a nuna cewa ana tare da Ganduje. Tir!

An cuce ka ana nema maka hakkinka amma ka ka sa ganewa. Don Allah a irin wannan makarantu akwai 'ya'yan Ganduje ko wani jigon siyasa a Kano?

Ba ma ga yaransu ba, shin akwai 'ya'yan Ganduje a cikin malaman makarantun firamare? Ina tuni ya tura 'ya'yansa zuwa NCC suna aiki a can an barku da koyarwa a firamaren gwamnati kuma kuna yin masu bauta.

Wani daga cikin iyayen yaran nan Wanda a da can dan ga-ni-kashe-nin Ganduje ne ya turo mun sako kan abun nan da ya faru, inda ya ce mun wallahi 'yan siyasa suna cin masu zarafi, ya ce shi dai a yanar gizo ne kawai ya ga hoton dansa yana zanga-zanga, a cewarsa abun ya ba shi takaici, kuma ma ya roki Allah ya saka masu abun da aka yi masu tun daga kan malaman zuwa hukumomi.

Ni kuma na amsa masa da cewa amin, amma na kara da ce masa ai kadan ma kenan, sai an sanya yaran sun yi dangwalen zabe bayan sun gama an kuma bude masu wuta an kashe su tukuna zai yi babban Allah ya isa.

Daga karshe ina kira ga talakawa su fahimci cewa 'yan siy

No comments

Powered by Blogger.