5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 CBN Ya Kwace Lasisin Bankin Skye Nigeria Plc, Kwastomomi Zasu Koma Wani Sabon Banki - Arew@Blog CBN Ya Kwace Lasisin Bankin Skye Nigeria Plc, Kwastomomi Zasu Koma Wani Sabon Banki - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

CBN Ya Kwace Lasisin Bankin Skye Nigeria Plc, Kwastomomi Zasu Koma Wani Sabon Banki

CBN ya kwace lasisin bankin Skye Nigeria Plc, kwastomomi zasu koma wani sabon banki
Babban bankin Nigeria CBN ya kwace lasisin gudanar da aiki na bankin Skye Plc bayan da ya shafe shekaru biyu tana dagawa bankin kada akan wasu dalilai.
Gwamnan CBN, Godwin Emefiele a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Legas, ya ce:
“A matsayinmu na hukumar gudanarwar bankuna, kuma wadanda ba sa yanke hukunci sai mun tuntubi hukumar inshoran masu ajiye kudade ta kasa NDIC, zuwa yanzu mun yanke hukuncin kafa wani sabon banki da sunan ‘Polaris Bank’, don kwashe komai na bankin Skye.

CBN Ya Kwace Lasisin Bankin Skye Nigeria Plc, Kwastomomi Zasu Koma Wani Sabon Banki

 Ku Dakko Android App Dinmu Domin Saukin Dakko Waka Da Bidiyo 
 
 0 87
Get real time updates directly on you device, subscribe now.
- Advertisement -
CBN ya kwace lasisin bankin Skye Nigeria Plc, kwastomomi zasu koma wani sabon banki
Babban bankin Nigeria CBN ya kwace lasisin gudanar da aiki na bankin Skye Plc bayan da ya shafe shekaru biyu tana dagawa bankin kada akan wasu dalilai.
Gwamnan CBN, Godwin Emefiele a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Legas, ya ce:
“A matsayinmu na hukumar gudanarwar bankuna, kuma wadanda ba sa yanke hukunci sai mun tuntubi hukumar inshoran masu ajiye kudade ta kasa NDIC, zuwa yanzu mun yanke hukuncin kafa wani sabon banki da sunan ‘Polaris Bank’, don kwashe komai na bankin Skye.
- Advertisement -
“Ya ce:”Bayan gudanar da bincike musamman akan gudanarwar ayyukan bankin, mun sanar da cewa bankin Skye na bukatar kudade masu yawa idan har yana son ci gaba da aiki da kuma samun rance daga babban bankin kasa.
Amma masu saka hannun jari a bankin sun kasa samar da wadannan kudade
Idan za a iya tunawa a ranar 4 ga watan Yulin 2016, CBN ya dauki wani mataki akan bankin Skye Nigeria Plc, wanda ya zama silar murabus din shugaban bankin, da dukkanin kananan daraktocinsa gami da manajan darakta tare da mataimakinsa, da kuma wasu manyan daraktoci guda biyu da suka dade a hukumar gudanarwar bankin.
A hukuncin da CBN ya yanke yanzu, ana sa ran kamfanin da ke kula da harkokin kadarori na kasa AMCON zai samarwa bankin na Skye kudaden gudanarwa, tare da nemo masu saka hannun jari da za su sayi kadarorin AMCON.
Emefiele ya ce: “Don haka muke tabbatarwa wadanda suka ajiye kudinsu a bankin, da su kwantar da hankulansu, domin kudadensu na nan kuma hada-hadarsu za ta ci gaba a sabon bankin zuwa ranar Litinin,24 ga watan Satumba, 2018, don baiwa kwastomomi damar yin amfani da kudaden da suka ajiye a bankin.”

No comments

Powered by Blogger.