Yadda aka donut
Abubuwan hadawa
- Falawa kopi 3
- Bota 1
- Kwai 3
- Mangyada
- Suga rabin kofi
- Gishiri rabin cokali
- Yeast cokali daya
- Baking hoda cokali 1
Yanda ake hadawa
- Da farko zaki tankade fulawarki a kwano mai fadi.
- Sai ki sa yeast da baking hoda ki juya, sai ki sa bota ki yi ta juyawa ya hadu da fulawan sosai.
- Sai ki fasa kwanki ki zuba ki juya ya hadu da fulawan.
- Sannan sai ki zuba suganki a ruwan dumi ki juya sai ki zuba a fulawar ki kwaba da dan gishiri.
- Idan yayi sai ki rufe ki sa a rana yayi kamar minti arba'in.
- Sai ki duba idan ya tashi sai ki dora kaskonki a wuta kisa mangyada.
- Sai kuma ki kawo gwangwanin madara na ruwa don ki samu yayi rawun sai ki sa a paranti ki dinga murzawa kina sa wannan gwangwanin kina fitar da rawun din donut dinki, kuma ki na sawa a mai kina soyawa, hakan zaki yi tayi harki gama.
No comments