5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Wuraren ban sha'awa da za ku iya ziyarta a Najeriya - Arew@Blog Wuraren ban sha'awa da za ku iya ziyarta a Najeriya - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Wuraren ban sha'awa da za ku iya ziyarta a Najeriya

A yayin da ake hutun makarantu a Najeriya, a lokacin ne mutane da dama ke neman wajen zuwa domin shakatawa da iyalansu.
Abu daya da za ku saka a ranku shi ne kuna bukatar kashe kudi domin tafiya hutu.
Akwai wurare masu kyau a Najeriya inda za ku iya zuwa ku ga al'adu da yanayi kala-kala.
Wadannan wasu wuraren shakatawa ne da za ku iya zuwa tare da iyalanku a lokacin wannan hutun.
1. Gandun namun daji na Lekki da keLagos
Wannan gurin shakatawar yana Lekki ne a Legas kuma gurin ya kai shekaru 21 yana tashe.
Wurin ya kuma kunshi birai da masu neman tsokana. Za kuma ku ga dawisu - in har kun ci sa'a - zai iya bude maku gashinsa. AbIn da ya fi burge mutane a wurin shi ne wani rufin bishiyoyi da ya kasance mafi dadewa a Afirka.
2. Kajuru Castle a KakeUmuahia

Kajuru Castle wani kasaitaccen gida ne da aka gina mai tsari irin na Turawa a garin Kaduna da ke Najeriya.
An gina kasaitaccen gidan tun shekaru 30 da suka wuce.
Dakunan gidan sun yi kama da kurkuku irin na zamanin da, kuma akwai wani rami da aka ajiye kada. Gidan na dauke da wurin ninkaya da na wankan sauna.
3. Gidan ajiye kayan tarihi na yaki da keUmuahia
Idan kuna son sanin wani abu kan yakin basasa a Najeriya, wannan ne wurin da ya kamata ku je. Wannan gidan adana kayan tarihin na garin Abia, kuma yana da dakuna 3 da ake baza hotunan tarihi. Akwai kuma dakin adana hotunan yakin basasa, da na hotunan sojoji, da kuma na hotunan kayan tarihin yaki.
4. Gidan namun daji na Jos
Wannan gidan ajiye namun daji ne a garin Jos. Garin na daya daga cikin manyan garuruwa a Najeriya da ake ajiye namun daji daban-daban kamar giwaye, da zakuna, da birai, da kadduna, da kuma wasu namun dajin. Jos Wildlife Park na budewa ne daga ranar Litinin zuwa Asabar a kowane mako, daga karfe 9 na safe zuwa 5 din yamma.
5. Wajen shakatawa da wasan yara naWonderland Amusement da ke Abuja
An bude wurin wasan yara na Wonderland a shekarar 2007.
Wannan shi ne babban wurin wasan yara a Najeriya kuma yana nan a daura da babban filin wasa na kasa a birnin tarayyar Najeriya Abuja.
Kuna bukatar ku cika cikinku kafin kuje wurin domin ku samu karfin iya hawan duka abubuwan wasan yaran da ke wurin.
6. Tafkin Oguta da ke ImBauchi

A jihar Imo za a sami tafkin Oguta. Wanan wurin shakatawa ne da za ka iya zuwa ka yi hutu, kuma ba ka ma bukatar kudi da yawa domin aji dadi a wanan wurin.
Wurin shakatawar yana da abubuwan yi da dama na jin dadi da za ka iya yi da iyalanka kamar ninkaya, da yawo cikin kwale-kwale, da kuma buga wasan golf.
7. Gandun namun daji na Yankari a Bauchi
Wannan gandun namun daji ne a jihar Bauchi, kuma shi ne wurin da aka fi zuwa domin shakatawa a Najeriya.
Ba namun dawa ne kadai a wurin ba har da koramar ruwan dumi ta Wikki. Ku da iyalanku ko abokanku na iya kama daki domin kwana a wurin.

No comments

Powered by Blogger.