Osinbajo ya ba da umarnin a yi wa SARS garambawul
Mukaddashin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo, ya bayar da umarnin yin garam bawul wa hukumar gudanarwa da kuma ayyukan rundunar 'yan sanda ta musamman ta yaki da fashi da makami (SARS).
Mukaddashin shugaban Najeriyar ya ba da umarnin ne bayan korafe-korafen take hakkin bila Adama da aka yi wa rundunar yaki da fashi da makami (SARS) din.
Cikin 'yan kwanakin nan dai matasa a Najeriya sun yi ta neman a soke rundunar a shafukan sada zumunta, musamman ma Twitter ta hanyar amfani da maudu'in #EndSARS .
Wata sanarwa da babban mai taimakawa na musamman na mukaddashin shugaban kasar kan harkar watsa labarai, Laoulu Akande ya fitar, ta ce duk wata rundunar da za ta fito bayan garam bawul din za ta mayar da hankali ne kawai kan aiki da bayanan sirri da hanawa tare da gano fashi da makami da satar mutane, gami da kama wadanda da suka yi irin wadannan laifukan.
No comments