''Mun kashewa ofishin mataimakin gwamna sama da miliyan 120''
Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da karbar wasikar barin aiki da mataimakin gwamnan jihar Farfesa Hafiz Abubakar ya gabatar mata.
Gwamnatin ta musanta wadannan zarge-zarge inda ta ce babu wani sabani ko bi-ta-kulli da ake yi wa tsohon mataimakin gwamnan.
A wata sanarwar da ta fitar, gwamnatin ta ce a 2017 kadai, Naira miliyan 120 aka kashe wa ofishin mataimakin gwamnan na alawus din tafiye- tafiyensa. A 2018 kuma an kashe ma sa Naira miliyan 30.
A baya-bayan nan dai tsohon mataimakin gwamnan ya bayyana a wata hira da BBC cewa tsawon fiye da shekara biyu suna zaman doya da man ja tsakaninsa da gwamnan Kano.
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar ya yi murabus bayan an shafe watanni ana takun saka tsakaninsa da gwamnan.
Mataimakin gwamnan ya sanar da murabus din nasa ne a wata wasika da ya mika ma gwamnan jihar Dr. Abdullahi Ganduje.
A cikin wasikar, ya ce ya so ya cigaba da rike mukamin mataimakin gwamna har zuwa karshen wa'adin mulkin da aka zabe su, amma ya sauka ne saboda matsalolin da suka dabaibaye dangantakarsa da gwamnan jihar:
"Ina sanar da kai cewa na yanke shawarar sauka daga mukamin mataimakin gwamnan jihar Kano daga ranar Asabar 4 ga watan Agusta, 2018.
A cikin wasikar, ya kara da cewa, "Idan baka manta ba mai girma gwamna, na sha jan hankalinka ga wasu batutuwa da ka iya tada husumar da muke fuskanta a yau, amma kokarin nawa bai yi nasara ba."
Kwamishinan watsa labarai na jihar Kano, Muhammad Garba, ya tabbatar da aukuwar wannan lamarin.
A wata hira da yayi da BBC, kwamishinan ya ce mataimakin gwamnan ya mika takardar barin aiki a fadar gwamnatin jihar Kano.
"Na bincika, kuma na tabbatar da cewa ya gabatar da wannan takarda a gidan gwamnati a yau din nan, kuma mun duba takardar da abin da ta kunsa."
Kwamishinan ya kara da cewa, "Abin da yake nunawa shi ne cewa ya bar aiki a matsayinsa na mataimakin gwamnan jihar Kano."
Da aka tambaye shi ko gwamnan jihar Kano ya amince da wannan mataki na mataimakin nasa, sai Kwamishinan ya ce:
"Mai girma gwamna na nazarin wannan takarda."
A baya bayan nan ne mataimakin gwamnan ya rubuta wata wasika ga hukumomin tsaron Najeriya, inda yake neman da su dauki mataki akan abin da ya kira wata barazana da jami'an gwamnatin jihar Kano ke yi ga lafiyarsa.
No comments