Matashi ya kirkiri na'urar rage barnar abinci a Afirka
Barnar abinci matsala ce da ake fama da ita a duniya baki daya.
A Afirka kadai, abincin da ake barnatarwa duk shekara zai iya ciyar da mutum miliyan 300.
Amma wani dalibi a Uganda ya kirkiri wata fasaha wacce za ta magance wannan matsala a kasarsa.
Wannan labari na daga cikin shirin BBC na masu Fasahar Kirkira wato BBC Innovators, wanda Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta dauki nauyi.
No comments