5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Kani ya doke yayansa a zaben cike gurbi na Daura - Arew@Blog Kani ya doke yayansa a zaben cike gurbi na Daura - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Kani ya doke yayansa a zaben cike gurbi na Daura

Ahmad Babba Kaita na APC ya doke dan uwansa Kabir Babba Kaita na PDP
Dan takarar jam'iyyar APC Ahmad Babba-Kaita ya doke dan uwansa Kabir Babba-Kaita na PDP a zaben cike gurbi na dan majalisar dattawa da aka gudanar a Katsina ta arewa a ranar Asabar.
Hukumar zabe ta ce Ahmad Babba-Kaita na APC ya samu kuri'u 224,607, yayin da Kabir Babba Kaita na PDP ya samu kuri'u 59,724.
'Yan uwan biyu sun fafata ne domin cike gurbin marigayi Sanata Mustapha Bukar wanda ya rasu a farkon watan Afrilun bana.
An dai gudanar da zaben lafiya ba tare wani tashi hankali ba duk da zaben na 'yan gida daya ya ja hankali a Katsina da ma Najeriya baki daya.
Hukumar zaben a Najeriya ta gudanar da zaben cike gurbi na 'yan majalisa a jihohi guda hudu da suka kunshi Katsina da Kogi da Bauchi ta kudu jihar Cross Rivers.
Sai dai kuma zaben jihar Kogi ya bar baya da kura inda rahotanni suka sun nuna cewar an samu matsalar satar akwatunan zabe da har ya janyo rasa rayuka.
Rikici da Matsalar satar akwatunan zabe da sayen kuri'u ne rahotanni suka ce suka mamaye zaben cike gurbi na dan majalisar tarayya da aka gudanar a jihar Kogi.
Rahotannin sun ce mutum biyu aka kashe a lokacin da ake zaben cike gurbin na dan majalisar Tarayya da ke wakiltar Lokoja/Kogi da Koton Karfe.
Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar wa kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN cewa an kashe mutanen biyu ne yayin da suka yi kokarin satar akwatunan zabe.
Akwai runfunan zaben da kuma rahotanni suka ce 'yan bangar siyasa sun hana gudanar da zaben.
A jihar Bauchi kuwa, 'yan takara tara ne ke neman darewa kujerar sanatan gundumar kudancin jihar.
'Yan takarar sun hada da Lawal Yahaya Gumau (APC), sai Isah Yuguda (GPN), sai Haruna Ayuba (ADC), da Aminu Tukur (APP) da kuma Usman Hassan (Kowa Party).
Sauran sun hada da Maryam Bargel (SDP) da Husseini Umar (NNPP) da Usman Chaledi (PDC) da kuma Ladan Salihu (PDP).
A jihar Cross Rivers da ke kudu maso gabashin Najeriya kuwa, an gudanar da zaben dan majalisar jiha mai wakiltar mazabar Obudu ne.
Mazabar ba ta da wakili tun bayan mutuwar wakilinsu Mista Stephen Ukpukpen a karshen watan Mayun bana.
Tuni dai aka gudanar da zabubbukan kuma a halin yanzu ana dakon sakamako ne a wadannan mazabu a sauran jihohin da aka gudanar da zaben cike gibin.
Hukumar zaben Najeriya ta bayyana cewa wadanda suka kada kuri'unsu sun zarce mutum miliyan biyu a cikin kanana hukumomi 22 na jihohi hudun.

Zabukan da aka gudanar ranar Asabar

  • Zaben sanata a gundumar arewacin jihar Katsina
  • Zaben sanata a gundumar kudancin jihar Bauchi
  • Zaben dan majalisar wakilai a mazabar Lokoja-Kogi na jihar Kogi
  • Zaben dan majalisar jiha na mazabar Obudu a jihar Kuros Riba

No comments

Powered by Blogger.