Gwamnatin Kaduna za ta bawa teloli kwangilar dinki
Gwamnatin jihar Kaduna a arewacin Najeriya ta ce za ta bai wa teloli a jihar kwangilar dinkin kayan yara 'yan makaranta ga teloli a jihar.
Gwamnatin ta wallafa a shafinta na Twitter cewa duk telan da ke son samun kwangilar zai iya tura wa gwamnati bukatar hakan ga ma'aikatar ilimi ta jihar.
Wannan ne dai karo na uku da ake bai wa teloli irin wannan kwangilar.
Wani tela a jihar Alkasim Rabiu ya bayyana cewa sun yi farin ciki da matakin na gwamnatin.
Sai dai ya ce suna fatan wannan karon za a bai wa teloli kwangilar ne kai tsaye, ba ta hannun 'yan siyasa ba kamar yadda ya yi zargin cewa an yi a baya.
"A baya 'yan siyasa aka ringa bai wa wannan kwangila, kuma suka ringa karbar kudi daga teloli kafin su ba su, sannan an dauki tsawon lokacin kafin a kammala biyan teloli ladan aikin su," in ji shi.
To sai dai kakakin gwamnatin jihar ta Kaduna Samuel Aruwan ya ce, gwamnati ta dauki matakai don kaucewa matsalolin da aka fuskanta a baya.
Ya ce hakan ce ma ta sa aka nemi sai kowane tela ya "bayar da lambar asusun bankinsa, da kuma lambar BVN a matsayin sharadin samun kwangilar."
Ana san ran dubban daruruwan kaya za a dinkawa 'yan makarantar gwamnati a jihar a wannan karon.
Mista Aruwan ya shaida wa BBC cewa gwamnatin jihar za ta ba da kwangilar ne ga matasa don karfafawa sana'o'insu.
Tuni dai wasu teloli a Kaduna suka fara bayyana farin ciki dangane da wannan mataki na gwamnatin jihar.
No comments