5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Dandalin Kannywood: Abubuwan Ban Mamaki 5 Da Baku Sani Ba Game Da Jaruma Hadiza Gabon - Arew@Blog Dandalin Kannywood: Abubuwan Ban Mamaki 5 Da Baku Sani Ba Game Da Jaruma Hadiza Gabon - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Dandalin Kannywood: Abubuwan Ban Mamaki 5 Da Baku Sani Ba Game Da Jaruma Hadiza Gabon

Ko shakka babu Hadiza Gabon yanzu a iya cewa tana daya daga cikin matan da suka shiga harkar fina-finan Hausa ta masana’antar Kannywood suka kuma yi fice sosai ta yadda ko yanzu kasuwa ta watse, a iya cewa dan koli ya ci riba.

Jarumar dai ta shahara sosai inda ta fito a fina-finai da dama tare da lashe kyaututtuka ba iyaka tun bayan shigowar ta harkar fim shekaru kadan da suka wuce.

Haka zalika jarumar saboda kwarewar ta da kuma bajintar ta, hakan ne ma ya sanya ake saka ta cikin jerin fitattun mata a harkar fim din da suka fi karbar kudi kafin su taka rawa a fim din. NAIJ.com ta yi dogon nazari game da jarumar, ga kuma wasu abubuwan ban mamaki da muka tattaro maku game da jarumar:
1. A cikin shekara daya kacal jarumar ta koyi yaren Hausa har ta kware don ta shiga fim.
2. Yanzu haka jarumar na jin yare hudu(4) da suka hada da Hausa, Turanci, Faransanci da kuma Fulatanci.
3. Ta ce ta shiga harkar fim ne don ta samu kudin kafa gidauniyar taimakawa nakasassu wanda tuni ta cika burin na ta.
4. Sabanin da yawa daga cikin ‘yan matan fim, Hadiza Gabon ta taba yin fim din turanci.
5. Mahaifin ta dan asalin kasar Gabon ne amma kuma mahaifiyar ta ‘yar Najeriya ce.

No comments

Powered by Blogger.