Custom Sun Kama Mota Ma Dauke Da Harsashi Dubu Dari Biyu 200,000
HUKUMAR CUSTOM SUNYI BABBAN KAMU
Daga Datti Assalifya
Jami’an hukumar fasa kwauri ta Kasa wato (Custom) reshen jihar Nigeria, Kwara da Kogi sun kama wata babbar mota mai dauke da rejistan jihar Lagos AKD 904 XE makare da harsasai dubu dari biyu (200,000) ana kokarin shigu dasu Nigeria daga jamhuriyar Kasar Benin
Wanda yayi dakon harsashen sunanshi Martin Anokwara, an kamasu ne a tsakanin bodar Wawa-Babana a jihar Niger jiya Litinin da misalin karfe uku na dare, sunyi batan dabo wajen boye harsashen ta hanyar daura jarkoki a cikin motar ashe harsashi suka boye bayan anyi wa motar kwakkwaran bincike
Kullun ana yiwa ‘yan Nigeria mugun tanadi wajen shigo da kayan ta’addanci daga Kasar Benin, wai shin laifin me muka yiwa Kasar Benin ta bari ana shigo mana da kayan ta’addanci haka ba kakkautawa?
Muna fatan humomin tsaro zasuyi kwakkwaran bincike wajen zakulo duk wanda yake da hannu a shigo da wannan kayan ta’addanci su fuskanci hukunci sannan a bayyanawa ‘yan Nigeria sunayensu
Muna rokon Allah Ya kara tona asirin ‘yan ta’adda da wadanda basa kaunar mu zauna lafiya a Nigeria.

No comments