AISHA TALBA( TRUE LIFE STORY )
..
..
..
..
:::: Chapter 1
..
..
::
Sunana Berpperrh Shamakin Zazzau, kuma a
yanzu Shekaruna 24 abisa al'ada dolane arayuwa
mutun sayya fuskanta wata 'yar chakwakiya,
kamar dai yadda arayuwata na fuskanci wata
babbar chakwakiya wadda hakan ta canja man
rayuwa,
To atakai dai musoma daga farkon zancen,
.
Shekaranmu daya da wata biyar muna charting
da wata yarinya mai suna Aisha Mu'azu Aliyu
Babangida,
nida ita munshaku da juna sosai tana
mahaukacin sona before muhadu kwatsam sai
wata rana ta kira ni a waya dana dauka na ce,"
"Hello Gimbiya ta ina fatan kina cikin koshin
lafiya?
tayi murmushi ta ce," "Lafiya klau baby na, ina
fatan kaima zanji haka daga gare ka?
Nayi murmushi na ce," "Ai daga jin muryata ya
kamata ki fahimci hakan,"
"Naji dadi kasan me nake so dakai yanzu?
Na gyara zama na ce," "a'a sai kin fada,"
Ta ce," "Kaga shekara daya kenan da watanni
muna tare amma banda muryar juna bamu ta6a
ganin fuskokin mu ba,"
Na ce," "To meya kawo wannan zancen rashin
ganin juna?
Tayi murmushi ta ce," "Kada kadamu bawani abu
bane kawai ina so ne muhadu da juna yau,"
Na fiddo ido na ce," "Haduwa kuma, to a ina?
Ta ce," "A Kpakungu cikin KOWA SCHOOL gobe
misalin karfe 12:00pm amma kafin nan ya kamata
kasan yarinyar da zaka hadu da ita,"
Na gyara zama domin kuwa zanji bakon abu
aguna tunda muke da ita banta6a sanin ita 'yar
waye ba kuma ban ta6a tambayar ta ba domin ni
don Allah nake sonta badan komi ba kuma bata
ta6a nuna man ita yarinyar me kudi ba ce, amma
kuma ni ban 6oye mata komi ba tasan cewa ni ba
dan masu kudin da za'azo agani ba ne amma
tasan muna da wadata sai na ce," "To ina jinki
gimbiya," Sai ta ce," "Kasan ni 'yar waye?
Na ce," "A'a sai kin fada," ta ce," "To ni 'ya ce ga
Dr Mu'azu Aliyu Babangida Talban minna wato
tsohon gomnan daya sauka,"
Sai nayi murmushi domin kuwa haduwa da irinsu
aguna ba abu bane bako," Sai tayi shuru ta ce,"
"Meyasa bakayi mamaki ba?
Sai na ce," "Nayi mamaki mana amma daga ta
ciki ne zan jira ki a kowa school din Allah ya
kaimu anjiman,"
Tayi murmushi ta ce," "Ameeeeen,"
mukayi sallama da ita nakashe wayana sannan
nafara nazarin yadda zan 6ullowa haduwarmu
amma dole naje mata ashigar girma,"
Na ciro wayata na kira Abokina Sameer ba
mujima dayin waya ba sai gashi ya shigo dakina
yazauna kusa dani ya ce," "Mutumina ya akai?
Na ce masa," "Lafiya lau yau zan hadu Aisha Dr
Alh mu'azu Aliyu Babangida Talban minna misalin
12pm,"
Sameer ya fiddo ido ya ce," "Kananufin yarinyar
Talba?
Na ce," "Eh amma ina so nayi mata shigar girma
kuma kasan gobe su daddy zasuyi tafiya shida
mummy zuwa yola bikin Kanin mummy kuma sati
daya zasuyi kuma kaga dole a mota zasuje,"
Yayi murmushi ya ce," "To basai kahau daya
daga cikin motocin ba,"
Na dan hararesa na ce," "Kai bana so naje mata
da motocin gidanmu ni dai na aro nake bukata
zan biya konawa ne indai zan fita kunya,"
yakalleni ya ce," "ba Matsala za'asmu aron amma
kowace mota ka bada 7,000 kaga guda biyar zai
kama 35,000 ya kace?
na mike cikin sauri na dauko masa 40k na mika
masa tare da cewa," "Kai hada na oil don haka ku
biya gidan mai amma tare zakuje kai da
abokanka kuma kafada masu yadda za'ai kada
suyi man raini agaban yarinyar nan kuma su
kwantar da kansu suyi biyayya,
ya tafi tare da cewa," "To Berpperrh,"
Tunda naga ya fita ni kuma nashiga bandaki
nawatsa ruwa sannan nafito, Farar shadda ce
riga da malun malun nasa ajikina na dauki kuma
farar hula nasa shaddar taji aikin wuta na fesa
turarukana masu kanshin tsiya,"
.
Misalin karfe 11:35am Sameer da Abokanansa
suka shigo da motoci farare kuma duk
kamfaninsu daya Mercedes ce masu kyau sukayi
parking a harabar gidanmu,"
Ya daga waya kira ni wanda dama zaune nake
ina jiransu, ina dauka ya sanar dani suna waje,
cikin sauri natashi nafito sai naci karo da salmah
ta kalleni ta ce," "La yaya ina zuwa?
Na harareta na ce," "Wani gu zani,"
har zan wuce ta ce," "To shi wurin baya da suna
ne da baza afada man ba?
najuya ko waigowa banyi ba na ce," "To dola ne
nafada miki wurin dazani kinga tafiyata nasakai
nafita nahadu dasu Sameer shida abokanansa su
hudu da Habeeb da kamal da Ameer da faruq sai
na biyar din wato sameer,"
Sameer yabude man mota nashiga gidan baya
muka wuce, abun gunan sha'awa idan kammu,"
Bamuyi minti goma ba sai gamu a kofar kowa
school hon mukayiwa me gadi ya bude gate din
muka shiga filine makarantar take dashi sosai
mukayi parking ba tare munfito ba kowannenmu
yana cikin mota yana dakon zuwanta musanman
ma ni nida namatsu da na ganta,"
AISHA TALBA ( TRUE LIFE STORY )
::
::
::
::: Chapter 2
::
::
::
Ba muyi minti bakwai da zuwa ba sai ganin wasu
motoci mukayi Morano Guda bakwai bakake
sunshigo cikin wannan makaranta kallon motocin
nan kawai nakeyi har saida sukayi parking daga
can side guda sai jinai hanjin cikin sun fara
kadawa nakasa fitowa nima ina jira ta fara
fitowa,
Kwatsam sai ga calling dinta ya shigo wayata na
yi picking na karata akunne tare da cewa," "Hello
gimbiya ta tun dazu nake ta jiranki amma shuru
kodai nakoma gida ne?
"Wani irin kakoma gidan bayan nima nashigo
wurin kaine cikin Marsendes din dake parke a
gun?
na ce," "Eh nine to ki fito mana?
"A'a kai kafara zuwa kuma kai yakamata kafara
fitowa don haka kafito kawai,"
tana gama fadar haka ta kashe wayarta na kalli
Sameer wanda dama shine ya tuko motar danake
ciki na ce masa," "Sameer fita da saurin ka bude
man kofa,"
Cikin sauri ya fito yazo saitin danake ya bude
kofar na ziro kafafuwa na kasa cikin kasaita
nafito cikin motar sameer yayi saurin kulle marfin
motar ya tsaya bayana ya dan sunkuyar da
kansa kasa sauran abokanan nasa suka fito
sukayi cirko cirko a bayana abun nikaina ya bani
sha'awa,"
Minti daya da fito wana sai wani security dayake
cikin motar dake gaba da wadda take ciki ya fito
cikin bakaken kaya yazo saitin kofar motar da
take ciki ya bude mata kofa ya koma gefe suma
sauran security duk sun fito sunzo sun tsaya gefe
da gefen kofar motar da take ciki can sai ga wasu
fararen mata kyawawa masu kyau hadaddu su
biyar sunfito daga motocin dake gaba da bayan
tata, suma sunzo suntsaya kamar yadda security
sukai, ni dai nasaka namujiya ina kallon kofar
motar da take abude wadda har yanzu banga
kowa ya fito daga cikinta ba,
can sai gani nayi an sakko da kafa daya daga
cikin wannan motar kafar dauke take da kunshi ja
mai kyan tsiya, lokaci guda nashiga tunanin
wannan kafar Wllh da ace zan samu wannan
yarinyar amatsayin matar aure to da duk daren
duniya idan mukazo kwanciya saina lashe kafarta
sau 99 kafin nabata hakkinta na aure,
can sai hankalina yadawo jikina naci gaba da
kallon wannan kafar can saiga Aisha Talba ta
bayyana surar jikinta afili ma'ana tafito gabaki
daya daga wannan motar, na kalleta sosai
fuskarta babu bille sai falli take taji kyau idan
kaganta farace sol kamar balarabiya tana da
tsayin hanci bakinta cas dan daidai dauke da
jambaki idanuwanta kuma manya duke da tozali
sannan tana da dan tsayi amma ba sosai ba,
Na kalleta ta kalleni sannan ta tunkaro inda muke
tsaye da murmushi takeyi amma kuma sai daga
baya naga ta murtuke fuska sai kace nayi mata
babban laifin ganin yadda naga tana kallo na,"
Ba tare da nakalli Sameer ba na ce," "Kai Sameer
ya naga tana tunkaromu ne da fuskar mazga kai
wllh inah mushiga mota mutafi kawai, sameer ya
ce," "A'a Allah ya kyauta ka kwarara zuciyarka ka
dake karkaji tsoron yi mata magana,"
bakowa zai gane magana mukeyi ba amma su
abokanan tafiyarmu sunji komai,"
.
Cikin kasaita da rangwada suka karaso inda
muke, wani kallo data wurgaman wllh sai da naji
dama marina tayi tsabar furgici ta kai minti biyu
tana kallon dressing dina sannan ta kalli fuskata
ta ce," "Wow Alhaji Berrpperrh Shamaki koh?
Na kalli kwayar idanuwanta na ce," "Eh,"
Ta 6ata rai ta ce," "Aikin banza an fada maka
kaburge nine shine ka kakwaso wadan nan
kazaman kun zo wai don kaburgeni koh?
to bara nafada maka sam bakayi man ba Idiot
hmm kasan me?
Raina ya 6ace domin banyi tsammanin haka daga
gareta ba nadakatar da ita daga cigaba da
maganarta na ce," "Ya isa haka domin bazan juri
jin wannan kalaman naki ba amma ina so kisani
wllh da ace wata ce ta fada man irin kalaman da
kikai man yanzu wllh da sai na yage mata harshe
don haka sai anjima duniya ai ba gidanmu bane
kema bana babanki bane Na barki lafiya,"
AISHA TALBA ( TRUE LIFE SOTORY )
..
..
..
.....
.....Chapter 3
..
..
..
..
Cikin 6acin rai najuya nakai hannuna zan bude
marfin mota Sameer yayi saurin kai hannunsa ga
marfin motar ya zageta nashiga na zauna
mutanan nawa kowa yashiga motar daya tuko a
70 muka fita cikin wannan makaranta kawayenta
sai kallonmu suke hadda juyowa nima naga
hakane ta mirro ita kau ko wai gowa batayi ba,
tatsaya gyam kamar wata dutse wasu tagwayen
hawaye suka gangaro mata akan fuska, an kasa
wadda zata tambayeta damuwarta acikin
kawayenta saboda gudun 6acin ranta,
Sai aka samu wata daga cikin kawayen nata da
Aisha take jinta kuma tasan yarinyar bata da
tsoro wajen fadawa Aisha Gaskiya koda kuwa
ranta zai 6ace ne ita kanta tana jindadin zama da
ita sunanta Ikilima,
Ikilima ta kalleta cikin takaici domin kuwa sunji
haushin wulakancin datayi man ta dan harareta
ta ce," "To maye kuma na zubar da hawaye
bayan kin fada masa abinda ke ranki hmmm ai
kin bamu mamaki gaye iya gaye hadadde duk da
cewa ba fari bane sosai irin naki amma
baza'akirasa baki ba ga gashin gira masu yawa
gashin kansa kuwa ya kwanta liplip da ka gansa
kaga bafullatani gashi Handsome guy kuma yana
da dan tsayinsa don dakadan zai fiki tsayi kuma
ya iya wanka ga la66a kamar tupper kuma........,"
"YA ISA, Aisha ce ta dakatar da ita da hannu, taci
gaba da cewa," "Yabon nasa ya isa hakanan ko
angaya miki bana sonsa ne to bari nafada miki
ina mahau kacin sonsa kawai wasa nake masa
amma yayi fishi ya tafi gashi ban san inda zan
samesa ba kuma nasan bazai kara daga wayata
ba amma dole kugano man gidansu muje, kuka
yaci karfinta Ikilima ta kama hannunta suka sata
a mota,
suka tafi,"
.
Zuciyata tafar fasa take domin ban ta6a jin irin
kalaman da Aisha tazo man dasu ba,"
a kofar gida muka tsaya na bude marfin mota
nafito suma abokanan tafiyar namu suka fito na
kalli Sameer na ce," "Sameer kuje kumaida masu
motocinsu ba'a bina bashi koh?
Sameer ya ce," "Eh Berrpperrh ba abinka,"
Na ce," "Okey to Sai mun hadu,"
Nayi masauran abokanansa godiya sosai domin
naji dadin abinda sukai man, suka shiga mota
suka wuce,
Wasu tagwayen hawaye suka hau gudana a
fuskata na tura gate nashiga adaidai wannan
time din dana shiga naci karo da Salmah zata fita
a mota Kiran Honda V6 jajir tunda naganta nayi
saurin goge hawayen dake ambaliya a fuskata
tazo kusa dani tadan tsaya ta sauke gilas a
hankali ta kalleni ta ce," "Yaya Sannu da dawowa,
na kalleta na ce," "Yawwa kanwa Ina zuwa?
ta ce," "Kawai zan fita yawo ne naga nikadaice
agidan,"
na dan fiddo ido na ce," "To ina su mummy suka
je,?"
Salmah ta ce," "Sun wuce Yola dazu dazun nan
bayan fitarka,"
"Amma ai da gobe ne tafiyar tasu kuma sai su
tafi yau kuma ba'a sanar dani ba,"
Salmah ta ce," "Nima ban san dalilin tafiyarsu
yau din ba amma daddy yana ta kiranka awaya
baya zuwa line busy sai suka wuce amma yabar
ATM dinsa yace nabaka shiya tafi da dayan kuma
ya ce kada kafitar da kudi batare daya sani ba
dole ka kirasa awaya idan zaka cira kudi,"
Na sauke nunfashi na ce," "Jeki adawo lafiya,"
tayi murmushi ta ce," "Allah yasa,"
ta wuce ni kuma acikin zuciyata na ce,"
"Ameeeeeen,"
AISHA TALBA, ( TRUE LIFE STORY )
..
..
..
..
.....
..... Chapter 4
..
..
..
..
Tunda nashiga daki kaina ya hau saraman domin
kuwa tun daga faruwan wannan abun naji jikina
ba dadi,
dakyar natashi nashiga bandaki nayi wanka hade
dayin alwala nazo nayi sallar Azafar dina na
kwanta ko abinci ban samu naci ba har aka kira
la'asar sannan nayi sallata nakoma na kwanta
tunane tunane kawai nakeyi,
can daga sama sama sai naji hon din mota da
alamu Salmah ce ta dawo,
banyi minti biyu dajin sautin hon din motar ba sai
jinai ta turo kofar dakina tashigo ta yaye gyalen
dake rataye a kafadarta ta kwanto saman kirjina
taga ko irin wasannan banyi mata ba ballan tana
nayi mata kiss din dana sabayi mata a goshinta
yayin data kwanto jikina,"
Ta dago kanta ta kalleni nima kallon nata nayi
naga jikinta duk ya mutu sai ta tashi ta zauna ta
kalleni ta ce," "Maza sukan fara fushi da
kannansu ba gaira ba dalili shin maye ra'ayinka
akan wannan maganar? yaya nah,"
Nayi shuru bance uffan ba, ta juyo kaina tana
facing dina ta dafa man kafafuwa wanda suke
kusa da kwankwason ta ta ce," "Yayana kafada
man me nayi maka domin shurun nan da kakeyi
dani wllh jinake kamar ina mutuwa ina dawowa
ne,"
Wasu hawaye suka gangaro a kuncinta masu
dumi na kalleta cikin fuskar tausayi domin
tadamu sosai nasa hannu nagoge mata hawayen
na ce," "Kada kidamu bakece silar 6acin raina va
kuma 6acin randa nake bazan saukesa akanki
ba,"
ta kara gyara zama ta ce," "To yanzu fada man
damuwarka yayana,"
na kwashe duk labarin abinda ya faru na fada
mata tun farkon haduwarmu a facebook har fara
ganin juna damukai har aron motoci danayi duk
na fada mata amma abun mamaki ga abinda
Salmah ta ce," "Wllh yaya kayi babban kuskure
da farkon haduwarku kafara mata karya baka
tunanin nan gaba Allah ya kara hadu kushaku sai
kuma ka gabatar mata da Yaya Sameer a
matsayin abokinka?
me kake tunanin zai faru? to tunanin da zatai
aranta cewa badan Allah kake sonta ba kashigo
rayuwarta da karya don kasameta daga karshe
bayan kasamu dukiya sai ka gujeta koh?
na fiddo ido domin kuwa ni kaina banyi tunanin
haka ba, kaji yarinya me tunanin manyan mutane,
na kalli salmah na ce," "Ayya kanwata banyi
tunanin dake kikai ba kuma babban kuskure na
shine karyar da nayi mata amma kuma danasani
keya ce,"
Salmah ta mike tsaye ta duko tayi man kiss a
kunci na sannan ta ce," "Yaya bari naje na yi
sallar la'asar," tana fadar haka ta fita,
ni kaina inajin dadin zama da kanwar nan tawa,
Bani da wata babbar kawa ko aboki daya wuce
kanwata domin kusan kowane sirrina tasansa
kuma idan abu ya faru dani itace takan fara sani
kafin wani yasani muddin ina gida to baka
rabumu tare don kowane time idan ba aiki take
ba to muna tare,"
.
Salmah bayan ta gama sallarta sannan ta zauna
saman gado tana tunani a cikin zuciyarta ta ce,"
"Dolane inje gidan su 'yar iskar Aishar nan wadda
taciwa yaya mutunci na kulla Abota da ita ko
nasamu tazo gidan nan don hakama yanzu ya
kamata nafara hada mata tarko barama naje
gidansu yanzu,"
tana gama wannan tunanin ta mike ta janyo
gyalenta ta shigo dakina ta ce," "Yaya bani key
din Marsendes 4matic dinnan zanje wani gu,"
na kalleta na ce," "Kije a motar da kika dawo
yanzu mana,"
ta dan ta6e baki ta ce," "To ai babu mai acikinta
badadewa fa zanyi ba,"
Na bude loka naciro mabudin na mika mata ta
amsa ta fita tare da man bye bye,"
AISHA TALBA, ( TRUE LIFE STORY )
..
..
..
..
..
.... Chapter 5
..
..
..
..
Salmah ta bude mota tashiga ta bata wuta
sannan ta fita batayi minti biyar da baro warta
gida ba sai gata a unguwar Talba tanade kan
motar kwanar gidan talba Layi ne kake ji tsit ko
gittawar yaro ko yarinya ko kasamu ledoji ko
karikitai irin na bola a a sam babu gidane
hadadde mai cike da na urar daukan mutun tun
shanyowar ta kwanar gidan Ikilima na kallon
motar a jikin wata makekiyar na ura wadda take
haska kowani shashi dake gidan amma banda
shashin mahaifinta amma duk wani lungu ko
sako tana kallonsa acikin na ura na urar babba
ce idan kaganta tarabu gida gida ko wani 6arayi
tana gani acikin na urar,
Ikilima tana ta kallon wannan motar amma bata
gane kowaye acikin motar ba kasan cewa motar
lilli6e take da tintik gashi ita kuma ta kulle motar
tako ina baka ganin rigarta ballan tana fuskarta,"
Salmah tayi parking a bakin gate ta zage gilas
awannan time din Ikilima ta ga fuskar salmah,
ita kau Aisha hankalinta baya kan wannan na
urar, latse latsenta kawai take awaya ta kaicin
abinda ya faru ya isheta shiyasa ta dauki waya a
matsayin abokiyar firarta,
Salmah ta kalli securityn ta ce masa," "Nazo
wajen Aisha ko zan iya ganinta,?"
Securityn ya ce," "Bari na tambayeta wata kila ko
tasan da zuwanki maye sunanki?
Salmah ta ce," "Sunana Ummusalmah,"
nan take securityn ya kira Aisha awaya data
dauka ya ce," "Hello ranki yadade wata yarinya
mai suna ummusalmah tazo ganinki ki kalli
fuskarta wata kila kiganeta,"
Aisha cikin 6acin rai ta ce," "Ina zuwa karka
yanke wayar,"
Aisha ta tashi ta danna wani madanni ajikin na
urar tayo Zooming din fuskar Salmah,"
Aisha ta kalli Ikilima ta ce," "Wow kinga wata 'yar
fulani nan shin kin santa?
Ikilima ta kalli fuskar Salmah sosai ta ce," "No
ban santa ba kawai kice ya barta ta shigo kiji
meke ta fiye da ita wata kila sabuwar kawa
zakiyi,"
Aisha ta danyi tsaki ta ce," "Mitswww dan Allah
kibar maganar shashancin nan ki barni naji da
damuwar dake gaba na gayen nan,"
Ikilima ta ce," "To Allah ya baki hakuri,"
Aisha ta maida wayar a kunnenta ta cewa
securityn," "Kabarta ta shigo kuma kanuna mata
side dina,"
"To ranki yadade ki huta lafiya,"
Securityn ya fadi haka tare da yanke wayar,"
Yabudewa salmah gate tashiga ya biyota a baya
tadan tsaya ta leko ta ce," "What?
yay tsaye tsaye ya nuna mata wani titi wanda
yayi hagu da hannunta ya ce," "Nan zaki karya
kwana da kin danyi tafiya zakiga titin ya shiga
6arayin hannun daman ki sai ki shigesa ki mikesa
zakiga wani gate a bude kishiga fallon da zaki
tarar agabanki to shine nata kina tura kofar falon
zakiga sauran kofofi to kimike kawai zakiga kofa
tana facing dinki to kishiga zaki sameta,"
Salmah ta jinjina kai ta ce," "Kutmelesi to sannu
tasa hannu a jakarta ta ciro 2000 ta basa yayi
godiya ya wuce itama wucewan tayi, ta gane
kwatancen sa ita kau Aisha ta zura na mujiya
tana ta kallon Salmah na tunkaro falon da take a
jikin na urar dake manne a jikin bangon,"
Salmah ta kutsa kan motar cikin sashin side nata
taga wurin parking taje tayi parking ta fito cikin
tafiyar kasaita tashigo falon da Aisha take,"
cikin Sallamarta ta tura kofar ta danna kanta ciki,
Mutun biyu ne aciki daga Aisha sai Ikilima sauran
kawayen nata tun a hanya suka sauka kowacce
ta wuce gida,"
Ikilima ta kalli Salmah ta nuna mata kujera tare
da cewa," "Kya iya zama ga gu,"
Salmah ta zauna sai jita an turo kofa wata 'yar
aikinsu ce tashigo dauke fa faranti lemuka ne
dauke da katuwar kaza akai, Aisha ta kalleta ta
ce," "Ije mata gabanta,"
'yar aikin nan ta ije wannan farantin din a gaban
salmah,"
Ikilima ta zuba mata lemu ta mika mata Salmah
ta ce," "A'a nagode,"
Suka gaisa amma ta kasa gane wacece Aisha
acikin 'yan matan nan,"
Aisha ta kalleta ta ce," "Bai war Allah maye
sunanki?
Salmah ta ce," "Ummusalmah,"
Aisha ta dan gyada kai ta ce," "To kinsanni ne?
annan time din ta gane cewa me magana ita ce
salmah, tunda idan kana da tunanin da lura
ayanayin dressing dinta zaka gane ita ce,
Salmah tayi shuru tana nazarin ta ina yakamata
ta 6ullo," Sai jin Voice din Aisha a kunnenta tana
cewa," "Meke tafe dake?
Ko kin sanni ne dama?
Salmah taji tambayoyin sun dan razana ta
musamman ma yadda taga kyawawan 'yan
matan nan guda biyu suna kallonta,
Salmah ta ce," "A'a ko daya,"
Aisha ta ce," "To meya kawo ki wurina?
Salmah ta dan sun kuyar da kanta kasa domin
takasa hada ido da ita sai ta ce," "Kawai nazo ne
nagaishe ki kuma idan badamuwa ina so zan
rinka kawo miki ziyara akai akai,"
Aisha tayiwa salmah wani matsiyacin kallo
salmah ta furgita ta ta ce," "Wllh dagaske nake,"
Aisha ta ce," "To wannanma zuwan dakikayi
nagode zaki iya tafiya,"
Salmah ta ce," "To amma........ Aisha ta daka
mata tsawa, "Ya isa haka bana dadewa ina
surutu dayawa zuwanki guna baya da amfani
awurina tashi ki fita,
salmah tayi jinkirin tashi ta daka mata tsawa,
"TASHI KIJE MANA,
No comments