TUNATARWA'Yan Uwa Musulmi Kada A Manta Da Daren Daren 'Lailatu Qadri'ABUBUWA 15 DA ALLAH YA FIFITA DAREN LAILATUL QADRI AKAN DUKKAN DARARE BAKI DAYADaga Aliyu Ahmad*1-Allah ya zabi wannan dare na lailatul Qadri, ya fifita shi ya daukaka shi cikin falala da daraja da daukaka akan dukkan sauran darare baki daya**2-Sanyawa wata sura daga cikin surorin Alqurani mai girma SURATUL QADRI* (Dan girmama sha'anin wannan Dare.*3-Allah ya girmama sha'anin wannan dare na Lailatul Qadri**4-Daren lailatul Qadri dare ne mai albarka mai yawa**5-A cikin Daren lailatul Qadri ne Allah ya saukar da Alqurani zuwa saman Duniya a baitul Izza**6-Aiyukan ibada a wannan dare ya fi alkairi da matsayi da falala akan dararen watannin dubu wanda babu daren lailatul Qadri**7-Wanda ya dace da wannan dare kuma ya yi ibada a cikinsa, ya sami alkairi mai yawa, wanda kuma ya yi asarar wannan dare, to an haramta masa alkairi mai yawa**8-Wanda ya raya daren da ibada yana mai imani da kwadayin samun lada,to an gafarta masa abinda ya gabata na zunubansa**9-Raya darare goma na karshen Ramadan dan dacewa da Daren Lailatul Qadri, yin hakan sunna ce ta Manzon Allah s.a.w**10-Manzon Allah S.A.W ya koyar da yin wannan addu'ar a cikin wannan dare don samun afuwa da gafarar Allah"*ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻚ ﻋﻔﻮ ﻛﺮﻳﻢ ﺗﺤﺐ ﺍﻟﻌﻔﻮ ﻓﺎﻋﻒ ﻋﻨﻲ**11-Mala'iku masu yawa har ma da Shugaban Mala'iku wato Mala'ika Jibrilu suna saukowa cikin wannan dare*Suna saukowa ne domin yin addu'a da nemawa bayin Allah da suke raya wannan dare da ibada gafara a wajen Allah.*12-Daren mai aminci da walwala tun daga faduwar rana har zuwa fitowar Alfijir**13-A cikin wannan dare ne Allah yake tsarawa da rubuta Arziki da Ajali da sauran al'amurar wannan shekara gaba daya**14-Shaidan da rundunarsa ba su iya fitowa dan yada alfasha ga dan Adam a cikin wannan dare**15-Nemn Daren Lailatun Qadri da kirdadonsa yana cikin shiriyar Annabi s.a.w* Allah ne mafi sani.*ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻚ ﻋﻔﻮ ﻛﺮﻳﻢ ﺗﺤﺐ ﺍﻟﻌﻔﻮ ﻓﺎﻋﻒ ﻋﻨﻲ
No comments