GUDUMMAWAR CIBIYAR JIN KAI NA SARKI SALMAN GA NIJERIYA
MANUFA
Dukkan musulmi yana sa ne da cewa addinin musulunci ya wajabta taimakon gajiyayyu da raunana da mabukata da wadanda ke cikin ibtila'i, da kiyaye alfarmar ran 'dan adam.
Domin sauke wannan nauyi, mahukunta da 'yan kasar Saudi Arabia suke da dabi'ar taimakawa bil adama a duk fadin duniya, ba tare da la'akari da addini ko jinsi ba. Dabi'ar taimako dabi'a ce da ta shahara da mutanen kasar Saudiyya (musamman a tsakanin mahajjata), sun ciri tuta wurin agaji da jin kai da taimako fiye da duk kasashen Larabawa da Musulmi da ma kasashe masu arzikin man fetur.
Saboda cimma manufar taimako, gwamnatin kasar Saudi Arabia ta kirkiro wannan cibiya maisuna "Cibiyar Bayar Da Tallafin Jin Kai Da Agaji Na Sarki Salman" a turance "King Salman Humanitarian Aid & Relief Centre, KSrelief", ta hanyar tsare-tsare da bayar da kayan agajin jin kai a duk inda ake da bukata a kasashen duniya, domin mutunta Bil' adam da rage asara da radadin talauci. Domin tabbatar da cimma wannan manufa, Sarki Salman Bn Abdul-Aziz ya zuba karin kudi Riyal Biliyan Daya (SR 1,000,000,000) a asusun gudanar da wannan cibiya, kari akan Riyal Biliyan Daya na musamman da ke cikin asusun cibiyar, domin taimakon jin kai ga mutanen Yemen.
An gina gudanar da ayyukan wannan cibiya ne domin cim ma taimakon bil adam.
TARIHI
An kaddamar da wannan cibiya ne a ranar 13/05/2015 a karkashin kulawa da shawarin Khadimul Haramaini Sharifain, Sarki Salman Bn Abdul-Aziz, mutumin da ke ta tarihin sanya hannu kai tsaye a cikin ayyukan jin kai da taimako tun a shekarun baya, musamman a lokacin da yake rike da matsayin Gwamnan Garin Makka. Wannan dabi'a ce ta ci gaba ta haifar da wannan cibiya.
A lokacin kaddamar da wannan cibiya mai babban ofishinta a babban birnin Riyadh, a karkashin gudanarwan babban jami'inta, Dr. Abdullah Bn Abdul-Aziz al-Rabi'a, wanda ya fara aiki da ma'aikata guda hamsin, zuwa yanzu (shekaru uku bayan kaddamarwa) wannan cibiya tana da ma'aikata a fadin duniya kusan mutane dari biyu.
NA GABA-GABA A DUNIYA
Kasar Saudi Arabia tana daga cikin na gaba-gaba a kasashen duniya da suka yi fice wurin bayar da tallafin jin kai da agaji, musamman ga yankuna da kasashen da ibtila'i ya afka musu (kamar: barkewan cuta, girgizan kasa, guguwa, yaki, wutar daji da makamantar su) da kasashen da suke cikin tsananin talauci.
Za a iya sanin haka idan aka yi waiwaye baya, aka yi la'akari da bukatar da Majalisan Dinkin Duniya (UN) ta gabatarwa membobinta daaa kasashen duniya na kudade kimanin Dalar Amurka dari biyu da saba'in da hudu (USD 274 million) domin asusunta na tallafin ayyukan taimako da jin kai. A bugun farko, gudumawar da kasar Saudi Arabia ta bayar na gaba dayan wannan kudi.
AYYUKA DA NASARORI
Daga kaddamar da ita zuwa yau, wannan cibiya ta gabatar da ayyukan taimakon bil adama da bayar da kayan jin kai a kasashen duniya guda talatin da takwas a mabambamtan nahiyoyi (Africa, Asia, Europe and South America). Wannan cibiya tana zartar da ayyukanta ne ta hanyoyi kamar haka:
i. Amfani da tsare-tsaren sa ido akan dukkan kayayyakin taimako da agaji.
ii. Amfani da tsare-tsaren kwararrun masana da abubuwan zirga-zirgan diban kayayyaki tare da hadin kai da mahukunta kasar da za a kai kayayyakin da cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyi masu zaman kan su a cikin kasashen da za a kai kayan taimakon.
iii. Ana tsara shirye-shiryen (programs) taimako da agaji ne gwargwadon aunawa da tantancewa da dacewan wadanda za a mika musu taimako da tallafi a zababbun wurare da suke da bukata. Kadan daga cikin abubuwan tallafi da taimako da wannan cibiya ke bayarwa sun hada da:
1. Kudade
2. Katifu
3. Barguna
4. Kafa Tantuna
5. Kayayyakin abinci
6. Kayayyakin karatu
7. Gudanar da tantuna
8. Kayayyakin sadarwa
9. Gyara da gina makarantu da ajujuwa
10. Kayayyakin kiwon lafiya da magunguna
Babban dalilin nasara da wannan cibiya ke samu shi ne, hada kai da yin ayyuka tare da cibiyoyin jin kai da taimako na kasa da kasa (international) da na yankuna (regional) da na cikin gida (local) a lokuta da wuraren zartar da ayyukan tallafin jin kai da agaji. Dalilin bin wannan tsari muka samu cim ma kaiwa ga isar da taimako wa miliyoyin mutane a duk fadin duniya.
KASASHEN DA SUKA MORI TALLAFIN KSrelief
1. Afghanistan
2. Albania
3. Algeria
4. Bangladesh
5. Benin
6. Burkina Faso
7. Cameroon
8. Comores
9. Djibouti
10. Eritrea
11. Ethioia
12. Gambia
13. Ghana
14. Honduraa
15. Iraq
16. Jordan
17. Kazakhstan
18. Kyrgyzstan
19. Lebanon
20. Maldives
21. Mauritania
22. Myanmar (Burma)
23. Nicaragua
24. Niger
25. Nigeria
26. Pakistan
27. Palestine
28. Philippines
29. Senegal
30. Somalia
31. Sri Lanka
32. Sudab
33. Syria
34. Tajikistan
35. Tanzania
36. Yemen
37. Zambia
38. Zanzibar
TALLAFIN JIN KAI GA NAJERIYA
Najeriya tana daga cijin jerin kasashen da suka cancanci tallafin jin kai da ayyukan taimako, kasantuwar tana da 'yan gudun hijiran cikin gida (IDP) wadanda rikicin ta'addancin Boko Haram a yankin Arewa Maso Gabashin kasar ya raba su da muhallan su. A ranar 5th/3/2018 tawagar wannan cibiya ta ziyarci garin Maiduguri a yankin Arewa Maso Gabas, inda ta ziyarci sansanonin 'yan gudun hijira ta yi ganin idon ga halin da suke ci.
A yayin wannan ziyara ne a ranar Litinin, 6th/3/2018 wannan cibiya da hadin gwiwa da Saudi Fund For Development a karkashin jagorancin Nasir Bin Mutlak Alsabi'i (Assistant Dirrector, Emergency Aid Development Of Saudi Arabia) da jami'an wannan cibiya kamar, Khalid Bin Abd Rahman Almani da Muhammad Bin Addida Alnamla, suka kawo kayan gudumawar kayyayakin agaji wa gwamnatin Najeriya na kimanin Naira biliyan uku da miliyan dari shida (N3.6billion), kimanin USD 10million. Gudumawar da ta kunshi kayayyakin da suka hada da: kayan abinci da abinci masu gina jiki da barguna da katifu da tantuna da magunguna da kayan fida (surgical kits) da kudaden ginawa/gyara makarantu da littafai da kayayyakin karatu.
A ranar 8th/3/2018 tawagar ta ziyarci Shugaban Kasar Najeriya, Muhammadu Buhari a Fadar Aso Rock Villa, inda ya yi jawabin godiya ga Khadimul Haramaini Sharifain bisa wannan gagarumin tallafi da jin kai ga 'yan gudun hijira a Najeriya irinsa mafi girma daga wata kasar wwje. Shi kuma jagoran tawagar, Nasir Mutlak ya yi godiyan tarban karimci da gwamnati ta yi musu, tare da ambaton kyakkyawan alakar da ke tsakanin kasashen Saudi Arabia da Najeriya da fatan ganin karshen fitinar ta'addancin Boko Haram.
Don karin bayani a duba: Daily Trust, March 6th, 2018
Marubuci: Muhammad A. Shu'aibu
No comments