Ko Cristiano Ronaldo karami na iya gadon mahaifinsa?
Idan har Ronaldo zai iya yin haka, to za a iya cewa dansa ma zai iya yin hakan.
Cristiano Ronaldo dai ya kasance dodon raga a rayuwarsa ta tamaula.
Dan wasan na Portugal mai shekara 33 yana cin kwallaye 50 duk kaka a Real Madrid a cikin shekara tara da ya shafe a kulob din, kwazon da wani bai taba yi ba.
A yayin da a yanzu ake ganin Ronaldo ya kai karshen ganiyarsa, mutane sun fara tunanin yadda duniyar tamaula za ta kasance ba tare da CR7 ba.
Ko yaya kwallon kafa za ta kasance ba tare da daya daga cikin 'yan wasan da ba a taba ganin irinsu ba?
To sai dai da alama dan wasan da ya lashe Ballon d'Or har sau biyar yana kokarin ganin ya samu wanda zai gaje shi ta hanyar dansa, Cristiano karami.
Duka shekarunsa bakwai, amma matashin Ronaldon ya fara nuna alamun kwarewa da kwazo.
Kuma idan aka yi la'akari da cewa yana samun horo ne na musamman daga mahaifinsa, to ba abin mamaki ba ne.
Ku dube shi a nan a tsakanin masu tsaron baya inda ya kwanta ya cilla kwallo a raga a lokacin da suke fafatawa a Bernabeu.
An dauki hoton karamin Ronaldon a lokacin da ya kwaikwayi kwallon da mahifinsa ya yi tsalle ya daki kwallon ta baya (acrobatic) a wasan Real Madrid da Juventus a gasar zakarun Turai.
Duk da cewa bai yi nasarar cin kwallon ba da ganin yadda ya dake ta, amma duk da haka Cristiano karami na kokarin tabbatar da ya gaji yadda mahaifinsa ke cin kwallaye.
Kuma ko a yanzu Cristiano karami ya nuna yana samun kwarewar da sannu a hankali za ta iya yin daidai da ta mahaifinsa.
Cristiano Ronaldo karami yana da wasu halaye da kwazo da fasaha irin na mahaifinsa.
Yana motsa jiki da horo sosai. Kuma ya kan yi hakan tare da mahaifinsa.
"Baba, ina son na kasance kamarka," kamar yadda Ronaldo ya taba rubutawa tare da wallafa hotonsa da na dansa a shafin Instagram suna nuna damatsa.
Mun gama shan ice cream, yanzu sai kuma aiki," kamar yadda Ronaldo ya wallafa a Instagram.
Ronaldo gwani ne a bugun fanareti a kwallon kafa, inda ya ci kwallo 100 a shekarun rayuwarsa a tamaula, don haka shi ne ya dace ya horar da dansa dabaru da koyon cin kwallo a raga.
Ronaldo ya shaida wa dansa cewa "Idan ka gaza cin kwallo, sai ka kara kwazo," a yayin da yake koya ma sa dabarun cin fenareti.
Karamin Ronaldon ya barar da fanareti biyu daga cikin uku da ya buga a gaban mahaifinsa.
Bayan cin kwallo kuma, Karamin Ronaldo ya kwaikwayi yadda ake murnar cin kwallo a raga.
A kullum dai 'yan wasan kwallon kafa suna nuna kimarsu ko a bayan fili, inda ake ganin suna saka tufafi masu tsada da motoci masu tsada.
Tuni Cristiano karami ya san dadin zama a cikin mota mai tsada da ta kai fam miliyan 2.15.
Kuma a kallum yana son yin hoto da mahaifinsa tare da sanin muhimmancin sanya tufafi masu tsada
Yanzu kalubalen da ke gaban Cristiano karami kafin ya kamo mahafinsa, shi ne lashe kyautar Ballon d'Or sau biyar tare da girke mutum-mutuminsa kamar yadda aka karrama mahaifinsa.
No comments