Kannywood: Babu Mace Mai Dadin Zaman Aure Kamar ‘Yar Fim – Ladidi
Sammam Masu karatu ko kun san shahararriyar jaurmar wasan kwaikwayon ta taba yunkurin shiga aikin soja kafin ta fara wasa?
A karanta firar duka a Taurarin Nishadi
Muna so mu ji cikakken tarihin rayuwarki
Ni dai sunana Ladidi Abdullahi An fi sani na da suna Tubeeless. An haife ni a Kaduna a wata unguwa da ake kira Sabon Gari Nassarawa, wato dirkania ke nan. Na yi Furamare wato a Nassarawa na kuma je makaratar gaba da Furamare.duk a Kaduna wato, ina gama sakandare aka yi min auren fari sai Allah bai yi zamana da mijin ba, sai muka rabu.
Daga nan sai na ji ina son yin aikin kaki, na je na sayi ‘form’ din aikin soja na ruwa na cika na ba da aka kira mu, na je duk abubuwan da ake yi na yi daga, baya ban sake bin ta kan shi kuma ba saboda oda wasu dalillai.
Yaushe kika fara fim din Hausa, da wane fim kika fara, kuma Me ya jawo ra’ayinki kika shiga?
Wata rana sai Rabi’u Rikadawa ya zo gida ya same ni ya ce min, ki zo mu je ki yi aikin fim, shi da Obina. Na ce musu ku je zan zo,
Amma sai na ki zuwa na neme su. Sai muka hadu da Zainab Abubakar muna hira ta ce min, ki zo mu yi aikin fim mana. Na ce mata zan bi ki. Ta ce, min, duk ran da za ta yi aikin za ta kira ni mu je mu yi tare. Na ce mata ba damuwa. kuma kafin nan, muna Hausa ‘drama’ a makaranta dama. Ran da Alfa ‘care’ zai yi wani fim sai ta ce na zo mu je.
Na ce mata to, muka je muka gana, sai shi ya tambaya da ma ina fim ne?
Saboda ya ga ba na kuskure. Daga nan sai na muka cigaba da zuwa N TA. Oganmu George ya ce,, na iya ‘drama’ ana ta sani. Daga nan kuma ’yan Kano suka zo Kaduna za su yi wani flm sai aka kira ni. Kafin nan mun yi wani flm wanda Rabi’u Koli ya sa Wada Rikadawa ya kira na yi, sai na ciga da aiki sai aka cigaba da kira na ina yi, shi ne. Sai dai na manta shekarar gaskiya. Nasiru Gwagwazo zai yi wani fim Balarabe da Balarabe dila ya kira ina Abuja ya ce na je Kaduna za mu yi wani fim. Shi ma Nasiru Gwagwazo ya kira ni, na ce musu ina zuwa nako zo muka yiFim din da na fara na Turanci ne, shi ne na Alfa ‘care’.
No comments