Nigeria: Za a kai 'micijin da ya hadiye N36m kotu'
Hukumar tsara jarrabawar shiga jami'a a Najeriya, JAMB, ta ce nan ba da jimawa ba za ta gurfanar da ma'aikaciyarta wacce ta yi ikirarin maciji ya hadiye N36m a kotu.
Kakakin huhumar Fabian Benjamin ya shaida wa gidan talabijin na Channels TV ranar Talata cewa yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike kan Philomina Chieshe bayan an dakatar da ita daga aiki.
Bai fadi ranar da za a gurfanar da ita a gaban kuliya ba.
Misis Chieshe ita ce jami'ar da ke kula da harkokin sayar da katin da ake duba sakamakon jarrabawar ta JAMB reshen jihar Benue.
Ta yi ikirarin cewa wani "hatsabibin maciji" ya shiga ofishin hukumar inda ya je wurin da ake ajiye kudi ya hadiye naira miliyan 36.
Mai magana da yawun JAMB ya ce ba ita kadai ce ta yi korafin cewa kudin sayar da katin sun bata ba, yana mai cewa akwai "wani daga cikin ma'aikatan da ya ce ya yi hatsari inda katunan suka zube amma daga bisani mun gano cewa an yi amfani da su."
A cewarsa, "JAMB ta kudiri aniyar kakkabe dukkan mutanen da ke cin hanci da rashawa shi ya sa ka ga ba a taba samun kudin shiga a hukumar kamar wannan karon ba."
Hukumar EFCC, wadda ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, ta aike da sakon Twitter inda take cewa ba za ta yi rahama ga macijin da ke hadiye kudi ba."
'Ana tsokaci kan batun'
Tuni wasu mutane suka bude shafin Twitter mai suna Macijin Nigeria, wanda ke aikewa da sakonnin arashi kan batun.
Kazalika masu amfani da shafukan zumunta sun yi ta bayyana mamaki game da yadda micijin ya hadiye miliyoyin naira.
Wale Adetona ya ce: "Wanne irin maciji ne zai shiga ofishin JAMB ya hadiye naira miliyan 36 ba tare da ya sari mai gadi ko ma'aikacin ofishin ba?
"Ina mamaki kan yadda micijin da ke jin yunwa ya je ofishin JAMB domin yin rijistar jarrabawa amma maimakon hakan ya hadiye naira miliyan 36 daga ofishinsu da ke Makurdi", in ji Mr Aye Dee.
BBC ta yi ta kokarin jin ta bakin hukumar EFCC kan ko zuwa yanzu wanne mataki ta dauka kan wannan batu, amma har zuwa lokacin rubuta wannan labari ba ta same su ba.
A Najeriya dai an sha samun yanayi daban-daban da kudin gwamnati ke yin batan dabo, amma a iya cewa wannan ne karo na farko da aka taba zargin wata dabba da dauke kudi.
No comments