2019: 'Batun tazarce ba shi ne a gaban Buhari ba'
- Ministan ya ce hauhawar farashin kayayyaki ya ragu da kashi 15 cikin 100 a watanni 11 a jere
Ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed ya ce maganar sake tsayawa takara ba shi ne a gaban Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ba a wani martani da ya yi ga tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo.
- Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya aike wa BBC ranar Laraba.A ranar Talata ne Mista Obasanjo ya rubuta wata budaddiyar wasika wadda ya ba Shugaba Buhari shawara kan kada ya sake tsayawa takara a zaben shekarar 2019.Jami'in gwamnatin ya ce wajibi ne a yaba wa Buhari kan abubuwa biyu cikin ukun da aka yi kamfe a kansu; wato yaki da cin hanci da rashawa da kuma yaki da masu tada kayar-baya.Har ila yau, ministan ya ce tsohon shugaban ya ce gwamnatin Buhari ba ta samu nasara ba a fannin tattalin arziki saboda shi ne na uku cikin jerin alkawurran da aka yayin kamfe.Daga nan ya ce yana ganin cewa aikace-aikacen Obasanjo ne ba su "ba shi sukunin fahimtar dimbin ayyukan ci gaban da gwamnatin Buhari take gudanarwa ba a halin yanzu musamman a fannin bunkasa tattalin arziki."Ministan ya kuma ce dukkan alkalumman da ake amfani da su wajen bayyana karfin tattalin arziki sun nuna cewa Najeriya na samun ci gaba.Hakazalika ya ce kasar ta fita daga matsin tattalin arziki ne ta hanyar amfani da shawarwarin da wadansu 'yan kasar suke ba ta.Bugu da kari, ministan ya ce hauhawar farashin kayayyaki ya ragu da kashi 15 cikin 100 a watanni 11 a jere.Ya ce fito tsarin amfani da asusu na bai daya wato (TSA) ya sa gwamnatinsu ta tara naira biliyan 108 kuma ya ce kasar tana adana fiye da naira biliyan 24 a kowane wata daga sabon tsarin.Jami'in gwamnatin ya ce sun samu naira biliyan 120 bayan sallamar ma'aikatan bogi. Haka dai ministan ya yi ta zayyana nasarorin da gwamnatin ta samu daya bayan daya a cikin sanarwar.
- Kan batun rikicin manoma da makiyaya ya ce gwamnatinsu a shirye take ta kawo karshen matsalar duk da cewa gadon matasar suka yi daga gwamnatin da ta gabace su, kamar yadda ya ce.Daga nan ya bukaci 'yan kasar da su ba su goyon baya don ganin an magance hakan.Game da batun tazarcen shugaban kuwa, ministan ya ce da gaske na wadansu 'yan kasar suna kiraye-kirayen neman ya sake tsayawa takara, yayin da wadansu kuma suke nuna adawarsu ga hakan."Muna ganin wannan batun zai iya raba hankalin shugaban a halin yanzu saboda ya dukufa a kowace sa'a don ganin ya magance dimbin matsalolin da suke ci-wa kasar tuwo a karya wadanda galibinsu gadonsu ya yi daga tsoffin gwamnatocin da suka gabata," in ji shi.Har ila yau ya ce ba su taba tunanin cewa tsohon Shugaba Obasanjo yana da wata manufa ba kan wasikar bayan ci gaban kasa."Mun karbi shawarwarinsa da zuciya daya kuma muna gode masa kan yadda ya samu lokaci duk da dimbin aikace-aikacen da ke gabansa ya rubuta mana wannan doguwar wasikar," in ji ministan.Ita ma jam'iyyar APC a martaninta yaba wa tsohon shugaban ta yi.Sai dai ta ce ba duka abubuwan da ya fadi ba ne a wasika ta yarda da su, musamman game da jam'iyyar da kuma gwamnatin Najeriya.Sakataren yada labaran jam'iyyar Malam Bolaji Abdullahi ya ce "ba gaskiya ba ne yadda tsohon shugaban ya yi watsi da tsarin jam'iyyun kasar duka.
No comments