5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Nigeria: An 'hana' Musulma zama lauya saboda ta sanya hijabi - Arew@Blog Nigeria: An 'hana' Musulma zama lauya saboda ta sanya hijabi - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Nigeria: An 'hana' Musulma zama lauya saboda ta sanya hijabi

A halin yanzu dai Firdaus ba za ta iya wakiltar kowa a kotu ba har sai makarantar horas da lauyoyi ta "kira ta"
An hana wata 'yar Najeriya da ta kammala karatun lauya zama lauya - mai iya aiki a kotu - saboda hijabin da ta saka wanda ake ganin ya saba wa dokar tufafin makarantar horars da lauyoyin kasar.
Shugaban makarantar horas da lauyoyi Isa Hayatu Chiroma ya shaida wa BBC cewa an hana Amasa Firdaus shiga dakin taron yaye lauyoyi ne saboda bata sanya tufafin da ya dace ba.
Ta ki ta cire hijabinta, tana mai cewa dole ta saka hular lauyoyi kan dan-kwalinta, in ji shafin intanet na Nigerianlawyer.com.
Rahotanni sun ce Firdaus ta bayyana matakin a matsayin wani abin da ya keta hakkinta na bil Adama.
A jihar Legas ma dai sai da aka kai maganar saka hijabi a makarantin sakandare kotuHakkin mallakar hotoGETTY IMAGES
Image captionA jihar Legas ma dai sai da aka kai maganar saka hijabi a makarantin sakandare kotu
Wata mata dai ta wallafa wani sako a shafin sa da zumunta na Instagram inda ta yi korafin cewa masu kula da lamuran dokar Najeria sun yi wa wata "'yar uwa" wariya tana mai amfani da maudu'in #justiceforFirdaus.
Tuni dai 'yan Najeriya suka yi ta tafka muhawara a kotu kan hana mai saka hijabin zama lauya.

No comments

Powered by Blogger.