5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Mu za mu sa Buhari ya sake tsayawa takara a 2019 – Malami - Arew@Blog Mu za mu sa Buhari ya sake tsayawa takara a 2019 – Malami - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Mu za mu sa Buhari ya sake tsayawa takara a 2019 – Malami

Shugaba Buhari bai bayyana matsayinsa ba game da zaben 2019
Ministan Shari'ar Najeriya Barista Abubakar Malami ya ce za su roki Shugaban Kasar Muhammadu Buhari don ya sake tsayawa takara a babban zaben kasar wanda za a yi a shekarar 2019.
Ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyara da ya kawo mana a ofishinmu na Landan kwanakin baya.
Sai dai babban lauyan gwamatin kasar ya ce shugaban bai sanar da su matsayinsa a kan hakan ba tukuna.
Haka zalika ya ce su a shirye suke su "roke shi da ya sake tsayawa takarar saboda ganin abubuwa na alkairi da shugaban ya faro a kasar sun wanzu."
Yayin da aka tambayi ministan ko zai amsa kiran nasu, ganin cewa su mukarrabansa ne.
Sai ya kada baki ya ce "za mu tsananta roko."
Game da batun talauci da al'ummar ke fama shi kuwa, ministan ya ce abubuwa suna "kyautatuwa" ganin yadda kasar ta fara yin karfi a bangaren noma.
Har ila yau ya bayyana cewa an samu ci gaba ta fuskar tsaro, inda ya ce "a baya ma ai ba batun talauci ake yi, batun rayuwa ake yi."
  • Latsa alamar lasifika a hoton da ke kasa don sauraron hirar

No comments

Powered by Blogger.