Mu tuna da 'yan gudun hijira a lokacin Kirsimeti- Fafaroma
Fafaroma Francis ya yi kira ga mabiya darikar katolika a fadin duniya da kada su yi watsi da halin da 'yan gudun hijirar da suka bar garuruwansu a dalilin tashin hankali ke ciki.
A wani taron jajibirin Kirsimeti a cocin Saint Peter's a birnin Vatican, shugaban ya kwatanta hakan da labarin Maryam da Yusuf wadanda su ka rasa wajen zama a Bethlehem a lokacin da Maryam ke nakudar haihuwar Annabi Isa (AS).
Fafaroma Francis ya ce akwai darasi kan labarin Yusuf da Maryamu, mun ga yadda aka tilastawa iyalai watsewa mun ga yadda aka tilastawa wasu miliyoyin mutane tserewa daga muhallan su.
A Bethlehem din yanzu an samu raguwar masu zuwa ziyara saboda karuwar tashin hankali tsakanin Falastinawa da sojojin Isra'ila.
Hakan ta faru ne tun bayan da Shugaba Trump ya ayyana Jarusalem a matsayin babban birnin Isra'ila.
No comments