5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Kannywood: Rahama Sadau Ta Sha Da Kyar A Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’Adua - Arew@Blog Kannywood: Rahama Sadau Ta Sha Da Kyar A Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’Adua - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Kannywood: Rahama Sadau Ta Sha Da Kyar A Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’Adua













Fittaciyar jarumar wasan  fina-finan Hausa wanda kuma ke fama da rikice-rikece a masana’antar a kwanakin nan, Rahama Sadau, ta sha da kyar a jami’ar Umaru Musa ‘Yar’Adua, dake Katsina bayan da wasu gungun daliban jami’ar suka yi kokarin murkushe ta a harabar makarantar da aka fi sani da ‘Students’ Centre’.

Rahotanni  sun shaida mana cewa shugabannin daliban jami’ar ne suka gayyaci jarumar domin su karramata a lokacin wani biki da suka shirya don tuna wa da ranar mata ta duniya.

Majiyarmu sun  bayyana mana cewa fitacciyar jarumar wadda tazo a makare a wurin taron bayan anyi nisa a ciki ta nemi wuri ta zauna ne a inda aka tanada domin ta kafin daga bisani a kira ta domin a bata shaidar karramawar da aka tanadar mata.

Tun farko dai rahotannin sun bayyana  cewa zuwan jaruma Rahama Sadau din ke da wuya sai kawai kallo ya koma mata yayin da wurin ya fara harmutsewa da lokacin da dliban jami’ar masoyan ta suka fara kokarin yin tozali da ita wasu kuma suna kokarin yin hotunan nan na dauka-da-kai watau (Selfie) a turance da jarumar.

No comments

Powered by Blogger.