5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Kanawa sun nuna wa mutanen Kudu yadda nake da gata – Buhari - Arew@Blog Kanawa sun nuna wa mutanen Kudu yadda nake da gata – Buhari - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Kanawa sun nuna wa mutanen Kudu yadda nake da gata – Buhari

Kanawa sun nuna wa mutanen Kudu yadda nake da gata – Buhari




Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce jama'ar jihar Kano sun nuna wa jama'ar kudancin kasar cewa har yanzu yana da gata.
Shugaban ya bayyana hakan a Kano lokacin da yake jawabi yayin da yake ziyarar kwana biyu.
Ya ce sun yi yakin neman zabe a shekarar 2015 a kan abubuwa uku wato: matsalar tsaro da batun tattalin arziki da kuma matsalar cin hanci da karbar rashawa.
Shugaba Buhari ya ce abin da ya fi ba shi wahala a tsawon mulkinsa na fiye da shekara biyu "shi ne hana yaki da cin hanci da rashawa."
Daga nan ya ba da labarin yadda ya yi yaki da cin hanci da rashawa yayin da yake jaorantar kasar a karkarshin mulkin soja wato a tsakanin shekarun 1983 zuwa 1985.
Ya ce yanzu ba zai iya yakar cin hanci da irin wancan tsohon salon da ya yi amfani da shi ba a wancan lokacin.

No comments

Powered by Blogger.