5882a97d3c9e7d2a39c31bf635c5b94f13333eda site-verification: 6fbe7c0858be540e9e5edfb8dbc755b0 Harry Kane ya kusa kai Alan Shearer yawan kwallaye - Arew@Blog Harry Kane ya kusa kai Alan Shearer yawan kwallaye - Arew@Blog

Header Ads

Header ADS

Harry Kane ya kusa kai Alan Shearer yawan kwallaye

Harry Kane ya ci kwallaon shi na farko a karawar Tottenham da Stoke ranar Lahadi
Ya fi Cristiano Ronaldo da Neymar da kuma West Brom da Crystal Palace - yawan kwallaye a shekarar 2017.
Iya zura kwallo a raga na dan wasan gaban Tottenham din ya ci gaba ranar Asabar inda ya ci kwallo biyu a wasan da Spurs ta lallasa Stoke da 5-1 a filin wasa na Wembley.
Kane ya ci kwallo 33 cikin wasannin gasar Firimiya 32, wadanda suke cikin kwallaye 50 da ya ci cikin wasanni 48 a dukkan gasa da ya buga wa kulob dinsa da kasarsa.
Dan shekara 24 din ya yi kusa da tarihin da mutumin da ake ganin Kane zai gada ya kafa- tsohon dan wasan gaban Blackburn da Newcastle da kuma Ingila, Alan Shearer.

No comments

Powered by Blogger.